Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 11:27:07    
Mutane 9212 sun rasa rayukansu a sanadiyar girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan na kasar Sin, gwamnatin kasar na yin iyakacin kokari don fama da bala'in

cri

Bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta yi an ce, ya zuwa yau 13 ga wata da karfe 7, girgizar kasar da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, ta haddasa mutane 9219 daga larduna da jihohi guda 8 suka rasa rayukansu, , kuma gidajen kwana fiye da dubu 50 sun ruguji.

Da misalin karfe 2 da minti 28 na jiya 12 ga wata da yamma, an samu girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Wannan girgirzar kasa tana da karfi sosai, kuma ta shafi yankuna da yawa. Bayan aukuwar wannan girgizar kasa, ba tare da bata lokaci ba ne, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da muhimmin umurni, inda ya nemi da a ceci mutanen da suka jikkata tun da wuri domin tabbatar da lafiyar jama'ar da wannan bala'i ya rutsa da su. Sannan kuma an kafa ofishin ba da umunin fama da bala'in girgizar kasa da ke karkashin jagorancin firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin. Yanzu firayin minista Wen Jiabao yana lardin Sichuan, don jarorancin ayyukan fama da bala'in.

Ya zuwa yau 13 ga wata da karfe 6, sojoji da 'yan sanda na musamman da suke aikin fama da girgizar kasa sun kai 16760, a waje daya kuma, sojoji da 'yan sanda fiye da 34000 suna kan hanyar zuwa yankuna masu fama da bala'in. Kazalika kuma, kungiyar fama da bala'in girgizar kasa ta gaggawa ta kasar Sin ta riga ta isa yankunan da ke fama da bala'in, don fara ayyukanta.

Bayan haka kuma, kwamitin kawar da bala'i na kasar Sin ya aiwatar da tsarin ba da amsa cikin gaggawa kan halin bala'in girgizar kasar da ake ciki. Bugu da kari kuma, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin, da ma'aikatar kudi ta kasar, sun bayar da kudi cikin gaggawa ga wuraren da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan. A waje daya kuma, ma'aikatar da ke kula da harkokin jama'a, da kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin sun kebe kayayyaki, don bayar da taimako ga mutanen da ke yankuna masu fama da bala'in da su warware matsalar zaman rayuwarsu. (Bilkisu)