|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-05-13 11:22:54
|
An soma yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Longyan na lardin Fujian
cri
Yau 13 ga wata da safe da karfe 8 da minti 12, an soma bikin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Longyan na lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin.
Birnin Longyan zango na karshe ne na bikin yawo da fitilar a lardin Fujian, tsawon hanyar da za a bi zai kai kilomita 30.5, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 208 . Za a soma bikin a filin jama'a na birnin Longyan, kuma za a kawo karshen yawo da fitilar a mahadar babbar hanya ta Longyan. A wannan rana da yamma da karfe 1 kuma, za a cigaba da bikin na tsawon kilomita 3 daga wurin taro na Gutian, kuma da karfe 3 saura minti 10, za a cigaba da bikin na tsawon kilomita 7 a gundumar Changting. (Bilkisu)
|
|
|