Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-12 22:08:08    
An kammala aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing a birnin Quanzhou da Xiamen cikin nasara

cri

Ran 12 ga wata, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing yadda ya kamata a birnin Quanzhou da birnin Xiamen na lardin Fujian da ke kudancin kasar Sin.

Yau rana ta biyu ce tun da aka fara mika wutar wasannin Olympics a lardin Fujian. Yau karfe 8 da minti 20 da safe, an fara mika wutar yola a birnin Quanzhou, birnin Quanzhou shi ne birni na babban yankin kasar Sin mafi kusa da Taiwan, kuma shi ne wani asalin mahaifa 'yan uwanmu na Taiwan. Mr. Wang Jiasheng mataimakin shugaban hukumar wasanni ta birnin Quanzhou ya zama mutum na farko wanda ya fara mika wutar.

A wannan rana da yamma da karfe 2, an fara mika wutar a birnin Xiamen birni mafi girma na biyu na lardin Fujian, kuma da karfe 5 da yamma, wutar ta isa cibiyar wasanni na birnin Xiamen, wurin karshe na wannan zango, kuma Ji Xinpeng 'dan wasan kwallon badminton wanda ya taba zama takara na wannan wasa ya mika wutar a karshe.