Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-12 21:17:46    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga wajen hukumomin noma da na kiwo na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin cewa, yawan kudin da jihar ta ware cikin shekaru 5 da suka wuce domin yin muhimman ayyukan noma da kiwo ya kai kudin Sin wato Yuan biliyan 2.3, sabo da haka sharudan aikin kawo albarka da zaman rayuwa na manoma da makiyaya sun kara samun kyautatuwa.

Jihar Tibet ta dauki matakai daya bayan daya domin kyautata aikin noma da kiwon dabbobi ciki har da kiyaye da kuma raya filin ciyayi na halitta, da shuka sha'ir mai inganci. Filin makiyayan da aka mai da su filin ciyayi ya kai kadada miliyan 1.75, kuma an haka ramukan gas wato methane a gundumomi 23 na jihar, ta yadda manoma da masu kiwo fiye da dubu 70 wadanda suke yin amfani da makamashi mai tsabta. Dukkan irin wadannan ayyukan da aka yi sun ba da kariya ga muhallin halittu na shiyyoyin noma da makiyaya na jihar Tibet, sa'an nan kuma sun kyautata sharudan aikin kawo albarka da zaman rayuwa na manoma da makiyaya sosai.

An ce, matsakaicin yawan tsabar kudin shiga da kowane manomi da makiyayi ya sumu cikin shekaru 5 da suka wuce ya karu da fiye da kashi 10 bisa 100 a kowace shekara.

---- Wani jimi'in ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin Sin kullum tana daukar aikin kiyaye harsuna da babbaku na kananan kabilun kasar a kamar harsashen kafa dangantakar kabilu bisa daidaici da hadin kai da taimakon juna da kuma jituwa, kuma ta samun tabbaci ga wannan aiki ta hanyar kafa dokoki.

A ran 11 ga wata a jami'ar koyon harsuna ta Beijing, an yi bikin murnar "shekarar harsunan kasashen duniya da ranar harsunan iyayen kasashen duniya a karo na 9", wakilai fiye da 100 da suka zo daga jami'o'i da kolejojin da abin ya shafa da ke wurare daban-daban na kasar Sin, da wakilan da suka zo daga ofisoshin jakadun kasashen Bangladesh da Poland da Jamus da Ingila da Australiya sun hallarci bikin.

A wurin budewar bikin, Mr. Zhang Qiang, mataimakin shugaban hukumar ba da ilmi ga kabilu ta ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, tsarin mulkin kasar Sin da sauran dokokin da abin ya shafa dukkansu sun tsai da cewa, kowace kabila tana da 'yancin bunkasa harshe da babbakunta.