Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-12 10:38:47    
Kasar Sin ta shiga cikin matakin hakika na aiwatar da aikin yin nazari da kera manyan jiragen sama masu daukar fashinja

cri

Saurari

A ranar 11 ga wannan wata a birnin Shanghai, an kafa kamfanin fitar da jiragen sama domin kasuwanci na kasar Sin kuma mai kula da harkokin yin nazari da kera manyan jiragen sama na daukar fashijoji, wannan ya bayyana cewa, kasar Sin ta shiga cikin matakin hakika na aiwatar da aikin yin nazari da kera manyan jiragen sama masu daukar fashinja. Firayim ministan kasar Sin Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, yin nazari da kera manyan jiragen sama zai kara daga matsayin kasar Sin wajen kimiyya da fasaha bisa babban mataki a dukkan fannoni.

A shekarar bara, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta ba da izni ga manyan ayyukan musamman na yin nazari da kera manyan jiragen sama masu daukar fashinjoji. Manyan jiragen sama masu daukar fshinjoji da kasar Sin za ta yi nazari da kuma kera su su ne, jiragen sama da ke zirga-zirga a manyan hanyoyi kuma za su iya daukar fashinjoji fiye da 100 a kowanensu. Kuma salonsu shi ne babban salon da kamfanin jiragen sama masu daukar fashinjoji na kasar Sin ke amfani da shi. Yanzu, a duk duniya, sai kasar Amurka da wasu tsirarrun kasashen da suka iya kera manyan jiragen sama masu daukar fashinjoji , kuma manyan jiragen sama da aka sayar da su a manyann kasuwannin duniya su ne jiragen sama mai kirar Boeing na Amurka da jiragen sama mai kirar Airbus na Turai kawai.

A gun taron kafa kamfanin jiragen sama na kasuwanci na kasar Sin, mataimakin firayim ministan kasar Sin Zhang Dejiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara sa kaimi ga yin nazari da kera manyan jiragen sama nmasu daukar fashinjoji. Ya bayyana cewa, ya kamata kamfanin kera jiragen sama na kasuwanci na kasar Sin yana tsayawa tsayin daka don yin sabbin kirkire-kirkire cikin 'yanci ba tare da tsangwama ba da kuma kara karfi ga samun manyan ayyukan fasahohi, kuma bisa shirin da aka tsai da don ba da tabbaci ga saurin yin nazari da kera manyan jiragen sama, a sa'I daya kuma, ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohi da sabbin kayayyaki da sauransu don mayar da manyan jiragen saman bisa matsayin da za su iya ba da tabbaci ga bukatun da aka yi wajen kwanciyar hankali da inganci da tattalin arziki da dadin da aka ji da kiyaye muhalli.

Mun sami labari cewa, kamfanin ya zuba jarin da yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 19, Mr Zhang Qingwei ya zama babban shugaban kamfanin. Ya bayyana cewa, bisa bukatun da aka yi wajen yin nazari da kera manyan jiragen sama masu daukar fashinjoji, mun riga mun tabbatar da muhimman fasahohi kusan 20 a fannoni 4 na tsara babban fasalin jiragen sama da makarraben injuna masu kwakwalwa a jere da harhada jiragen sama da neman shaidu ga dacewar zirga-zirgarsu domin kamfaninmu wajen yin nazari da kera manyan jiragen sama, mu ma za mu ci gaba da ba da taimakon juna tare da sauran ayyukan da za a yi ta yadda za a aiwatar da ayyukan yin nazari da kera manyan jiragen sama lami lafiya.

Bisa shirin da aka tsai da, an bayyana cewa, kasar Sin ta yi fatan za ta sami manyan jiragen sama masu daukar fashijoji da ita kanta ta kera kafin shekarar 2020, bayan kasar Sin ta yi nasarar kera manyan jiragen sama masu daukar fashinjoji, to za ta yi kokarin samun nasarar yin ciniki da manyan jiragen sama masu daukar fashinjoji ta yadda kamfanin kera manyan jiragen sama na kasar Sin za ta iya zama 'yar kasuwa da ke da karfin shiga gasar kera jiragen sama masu daukar fashinjoji a duniya.

A wannan rana, babban manaja na kamfanin Mr Jin Zhuanglong ya bayyana cewa, ya kamata mu yi la'akari da albarkatan zirga-zirgan jiragen sama da kasar Sin take da su a halin yanzu, a sa'I daya kuma, ya kamata muna ci gaba da aiwatar da manufar budewa kasashen waje kofa, kuma mu yi hadin guiwa da kasashen duniya cikin himma da kwazo. Wato, a lokacin da muke yin nazari da kera manyan jiragen sama, dole ne da akwai wasu 'yan kasuwa na kasashen waje da za su samar mana da danyun kayayyaki da injunan jiragen sama da sauransu. Wajen kwararru, muna maraba da kwararrun fannin nan na kasashen waje da za su shiga ayyukan raya zirga-zirgan jiragen sama na kasar Sin.(Halima)