Bisa labarin da muka samu daga kwamitin samun bunkasuwa da yin kwaskwarima na jihar Tibet ta kasar Sin, an ce, a cikin farkon watanni 3 na bana, jihar Tibet ta gudanar da manyan ayyuka cikin ruwan sanyi, kasar Sin ta zuba jari da yawansu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 3.6, wanda ya karu da ninki 8 bisa na makamancin lokaci na bara, wanda kuma ya kai matsayin koli a tarihi.
Kwamitin samun bunkasuwa da yin kwaskwarima na jihar Tibet ta kasar Sin ya ce, a cikin manyan ayyuka 180 da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tabbatar da gudanar da su daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, an riga an fara tsara shirinsu ko gudanar da su da yawansu ya kai 159.
Mataimakin zaunannen shugaban jihar Tibet Mr. Hao Peng ya bayyana cewa, makasudi na farko da ake gudanar da wadannan manyan ayyuka shi ne, domin kyautata zaman rayuwar manoma da makiyaya da kuma yanayin aikinsu.(Danladi)
|