Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 21:06:24    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa birnin Osaka, don cigaba da ziyarar aiki a kasar Japan

cri

Yau 9 ga wata, bayan da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kawo karshen ziyararsa a birnin Tokyo, ya isa birnin Osaka, don cigaba da ziyararsa a kasar Japan.

A lokacin ziyararsa a birnin Osaka, shugaba Hu Jintao zai gana da muhimman jami'an yankin Kansai, kuma zai halarci liyafar cin abinci da bangarori daban daban na yankin Kansai suka shirya, don maraba da ziyararsa a kasar Japan.

A wannan rana da safe a birnin Tokyo, shugaba Hu Jintao ya gana da manyan mambobin hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan da ke karkashin shugabancin Mr. Kono Yohei, shugaban majalisar wakilai ta kasar. Shugaba Hu Jintao ya ce, jam'iyyu daban daban na kasar Japan sun kawar da bambancin ra'ayoyinsu, kuma sun kafa hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan, wannan ya nuna kyakkyawan tunani na yada ra'ayin Olympics na jama'ar kasar Japan, da kuma zumuncin da jama'ar kasar ke nuna wa jama'ar kasar Sin.

A lokacin ziyararsa a birnin Tokyo, shugaba Hu Jintao ya halarci bikin nuna maraba da sarki Akihito na Japan ya shirya masa, kuma ya yi shawarwari tare da firayin ministan kasar Fukuda Yasuo, inda bangarorin biyu suka cimma haddadiyar sanarwa game da ciyar da dangantakar samun moriya ga juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Japan gaba. Bayan haka kuma, shugaba Hu Jintao ya yi jawabi a jami'ar Waseda, inda ya nuna cewa, yanzu dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan na kan sabun masomin tarihi, kuma tana fuskantar sabuwar damar kara samun cigaba. Kazalika, shugaba Hu Jintao ya halarci bikin bude shekarar yin cudanya da sada zumunta tsakanin yara manyan gobe da samari na kasashen Japan da Sin. Bugu da kari kuma, ya gana da shugabannin majalisar dattijai da na majalisar wakilai ta kasar Japan, da kuma shugabannin muhimman jam'iyyun siyasa na kasar, bayan haka kuma, ya yi hira tare da 'yan iyalan marigayi 'yan siyasa da abokai, wadanda suka bayar da taimakonsu kan sada zumunta a tsakanin Japan da Sin, da kuma wasu abokai na Japan. (Bilkisu)