Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 17:35:44    
Ziyarar da Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi a kasar Japan a ran 8 ga wata

cri
A ran 8 ga wata, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin kyakkyawar ziyarar aiki a kasar Japan ya halarci bukukuwa masu muhimmanci biyu da aka shirya a birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan.

A wannan rana da safe, shugaba Hu Jintao ya kai ziyara musamman ga kungiyar 'yan wasan ballet mai suna Matsuyama ta Japan, inda ya gana da tsoho Shimizu Masao da matarsa Matsuyama Mikiko wadanda suka dade suna kokari wajen yin ma'amalar al'adu a tsakanin Sin da Japan. Wadannan tsofaffi biyu wadanda yaransu ke rike da hannayensu sun tarye gaggan baki na kasar Sin.

A cikin daki mai tsabata inda ake horar da 'yan wasa, kuma a karkashin jagorancin Malama Morishita Yoko, shahararriyar 'yar wasan Ballet ta kasar Japan kuma surukar dan tsofaffin biyu, 'yan wasa sama da goma sun gabatar da wasa mai suna "Yabon Rawayen Kogi" musamman domin ziyarar da shugaba Hu Jintao ke yi. Cikin fuskantar iyalin Shimizu Masao wanda ke nuna wa kasar Sin babbar zumunta, Mr Hu Jintao ya bayar da jawabi mai cike da fara'a cewa,

"kungiyar 'yan wasan Ballet ta Matsuyama shahararriyar kungiyar 'yan wasan Ballet ce a duniya. Malam Shimizu Masao tsoho ne da ya dade yana kokarin dankon aminci a tsakanin Sin da Japan. A cikin sama da rabin karni da ya wuce, kun nuna imani ga sada zumunta a tsakanin Sin da Japan, kun yi kokari wajen inganta ma'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu, kun taka muhimmiyar rawa wajen kawo fahimtar juna da dankon aminci a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Da zuciya daya, nake fatan kungiyar 'yan wasan Ballet ta Matsuyama za ta kara samun yalwatuwa, kuma da zuciya daya nake fatan iyalin Malam Shimizu Masao da dukan aminamu na kungiyar Matsuyama za su ji dadin zama da koshin lafiya."

A shekarar 1971, bisa gayyatar da kungiyar 'yan wasan kwallon tebur ta Japan ta yi musu ne, 'yan wasa na kasar Sin suka shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur ta 31 da aka shirya a kasar Japan. Ta haka an gwada kyakkyawan misali ga yalwata hulda a tsakanin kasa da kasa ta hanyar wasan kwallon tebur. Haka kuma a shekarar 2006, kungiyar tsoffin gwanayen wasan kwallon tebur na kasar Japan sun kawo wa kasar Sin ziyara, don taya murnar ranar cika shekaru 50 da aka fara ma'amalar aminci ta wasan kwallon tebur a tsakanin kasashen biyu.

A ran 8 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayim minista Fukuda Yasuo na kasar Japan sun isa cibiyar ma'amalar duniya ta Jami'ar Waseda. A cikin babban daki, Wang Nan, shahararriyar 'yar wasa ta kasar Sin da Fukuhara Ai, 'yar wasa ta kasar Japan wadda jama'ar kasar Sin ke nuna mata kauna kwarai suna wasan kwallon tebur a tsakaninsu. Da ganin shugabannin biyu, sun yi farin ciki da kewayensu.

Fukuhara Ai, 'yar wasa ta kasar Japan wadda aka dade aka horar da ita a kasar Sin tana jin karin Sinanci iri na arewa maso gabashin kasar Sin. Mr Hu Jintao ya bayyana mata ta fuskar aminci cewa, "ke shahara sosai a tsakanin samari na kasar Sin."

Bayan haka Wang Nan, 'yar wasa ta kasar Sin ta gayyaci shugaba Hu Jintao don yin wasan kwallon tebur tare da su. Shugaba Hu ya yi farin ciki da amsa gayyatar. Da farko shugaba Hu da Fukuhara Ai, 'yar wasa ta Japan sun yi wasa a tsakaninsu cikin wasu mitoci, sai Wang Nan ita ma ta shiga cikinsu. Nan take shugaba Hu ya yi wasa a tsakaninsa da gwanayen wasan kwallon betur biyu na duniya. Wasan mai ban sha'awar da suka yi ya jawo hankulan samarin kasashen biyu sosai, sun tafa musu hannu don yaba musu.

Bayan da suka shafe mitoci sama da goma suna wasa, da zuciya daya, Mr Fukuda Yasuo, firayim ministan kasar Japan da ke kallon wasan, ya nuna yabo cewa, lale Mr Hu Jintao ya kware sosai wajen wasan kwallon tebur. (Halilu)