Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wato shirin musamman na murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.
Masu sauraro, idan mun ambaci sunan Amina, watakila wasu daga cikinku, musamman ma tsoffin masu sauraronmu?kuna iya tunawa da ita, sabo da ita malama Amina ta dade tana aiki a sashen Hausa.
Kasancewarta daya daga cikin ma'aikatan sashen Hausa na farko, ta gane ma idonta yadda aka kafa sashen Hausa, kuma ta kasance Basiniya mai watsa labarai ta farko a sashen Hausa. Yau shekaru fiye da 10 ke nan ta yi ritaya daga nan sashen Hausa, amma duk da haka, masu sauraronmu ba su manta da ita ba, har ma mu kan sami wasikun masu sauraronmu da ke mata gaisuwa.
Ga shi, kwanan baya, mun kai mata ziyara, kuma mun yi hira da ita. To, da farko, bari ta gabatar da kanta zuwa gare ku.
"Sunana Amina Li, na fara aiki a sashen Hausa tun daga watan Nuwamba, shekarar 1961, kafin in zo sashen Hausa, na taba aiki a sashen Faransa, cikin watanni uku kawai, bayan na gama koyo a kwalejin koyon harsuwan waje na Beijing."
Masu sauraro, kamar yadda kuka ji, tun farkon fari, malama Amina tana aiki ne a sashen Faransanci, kuma Faransanci ne ta koya a kwalejin koyon harsunan waje na Beijing. To, watakila yanzu akwai masu sauraronmu da ke shakkar, shin me ya sa daga baya ta yi aiki da sashen Hausa?
To, masu sauraro, kamar yadda kuka sani, a shekarun 1950 zuwa na 1960, kasashen Afirka da yawa na gwagwarmayyar neman 'yancin kansu daga kasashen da ke musu mulkin mallaka, kuma kasar Sin ta ji tausayinsu, ta kuma nuna tsayayyen goyon baya a gare su. A cikin irin wannan hali ne, a karshen shekara ta 1960, gidan rediyon kasar Sin ya fara shirin kafa sashen Hausa, don isar da goyon bayan jama'ar kasar Sin ga jama'ar Afirka da ke yunkurin neman 'yancin kansu.
Malama Amina ta tuna da cewa, "A lokacin nan, firaminista marigayi Zhou Enlai, ya gaya wa shugabannin rediyonmu cewa, ya kamata a karfafa hulda a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka, wadanda suke fama domin samun 'yancin kan kasarsu, wannan ya sa aka yi shirin kafa sashen Hausa da neman fara watsa labarai da harshen Hausa da wuri wuri."
Amma duk da haka, a lokacin, kusan ba wanda ya iya Hausa a nan kasar Sin, to, shi ke nan, yaya za a kafa sashen Hausa? Ashe, an gayyato wani masanin harshen Hausa mai suna Amada Bacha daga kasar Nijer, don ya koya wa wasu Sinawa harshen Hausa, kuma malama Amina tana daya daga cikinsu."
"Ina daga cikin mutane hudu wadanda suka kafa sashen Hausa, su mutanen hudu su ne malama Mairo, wato Li Xun, da malam Sa'idu(Zheng Jiachu) da malam Haruna(Wei Shaoqi) da kuma ni Amina(Li Xuan). Wannan masanin harshen Hausa ya kawo mana wani littafin Hausa, kuma sunan littafin (shi ne) 'ka yi karatu'. Kowace rana da safe, mun yi nazarin littafi tare da shi. Hanyarsa ta koyo kullum kamar haka, ya karanta kalma da kalma cikin Hausa, daga baya ya yi fassara da Faransanci. Da Sa'idu da ni Amina mu biyu mun kara fassara daga Faransanci zuwa Sinanci, domin sauran Sinawa biyu ba su iya fahimtar Faransanci ba."
Malam Amada Bacha babban masanin harshen Hausa ne, kuma ya ba da babban taimako ga kafuwar sashen Hausa, a yayin da take hira da mu, malama Amina ta nuna yabo da kuma godiya kwarai a gare shi.
"wannan masani mai suna Amada Bacha ya iya Hausa sosai, kafin ya zo kasar Sin, ya taba aiki a rediyon kasarsa wajen watsa labarai da harshen Hausa, ya kware sosai wajen watsa labarai, kuma ya shahara sosai a birnin Yamai, sabo da haka, ya ba da taimako sosai ga sashenmu, ko wajen koyar da harshen Hausa ko wajen yin fassara, kuma a wajen karanta labarai, shi ne ya koyar da ni wajen karantawa, don in zama mai karanta labarai na farko a sashen Hausa. Bayan zuwansa, dukan ma'aikatan sashenmu mun yi babban ci gaba wajen harshen Hausa"
Bisa kokarin da malamin da kuma dalibansa suka yi, sannu a hankali, malama Amina da dai sauran abokanta na karatu sun fara iya Hausa. Sabo da haka, a karshen shekarar 1962, sashen Hausa ya fara gwajin watsa labarai, kuma da Malama Amina da sauran ma'aikatan sashen Hausa, sun yi aiki, a yayin da suka kuma ci gaba da karatu.
malama Amina ta gaya mana cewa, "muna da mutane hudu ne kawai, fara watsa labarai da harshen Hausa, lalai, babban aiki ne mai nauyi gare mu, mun yi ta aiki dare da rana, da farko, mun koyi yaya za a fassara labarai daga Sinanci zuwa harshen Hausa, daga baya, mun rarraba aikin musamman ga kowa, alal misali, malam Sa'idu ya kula da fassara babban bayani na bayan labaru, malam Haruna ya koyi yadda za a amsa tambayoyin masu sauraronmu, ni dai ina kula da shirin faya-fayai."
A cikin watannin da sashen Hausa ke gwajin watsa labarai, malama Amina da sauran ma'aikatan sashen Hausa sun fara kwarewa wajen fassara labarai, ganin haka, shugabannin gidan rediyon kasar Sin sun tsai da kudurin fara watsa labarai cikin harshen Hausa a ran 1 ga watan Yuni na shekarar 1963 a hukunce. Ko kadan malama Amina ba za ta iya mantawa da wancan muhimmiyar rana ba. "Har abada, ba zan manta da wannan babbar rana ba. Domin tun daga safiyar ran 31 ga watan Mayu zuwa karfe 12 na dare a ran nan, mun yi aiki matuka, don gudun kuskure. Amada Bacha ya karanta labarai na minti kusan 15, bayan labarai, sai shirin fayafayai na minti 12 ko fi."
Wata daya bayan da sashen Hausa ya fara aiki a hukunce, sai ya sami wasika ta farko daga wajen masu sauraronsa. Daga baya, wasikun masu sauraro sun fara zuwa sashen Hausa kamar ruwan sama. "Galiban masu sauraronmu sun yi mana fatan alheri da nuna murnar bude sashen Hausa na rediyon Beijing, Sa'an nan, da yawa daga cikinsu sun yi mana zabi sonka, a cikin wasikunsu, wasunsu kuma suna son kulla zumunci tsakaninsu da rediyonmu."
Malama Amina ta shafe tsawon shekaru 36 tana aiki a sashen Hausa, kuma a karshen shekarar 1997, malama Amina ta yi ritaya, amma har kullum tana nuna kulawa sosai ga bunkasuwar sashen Hausa.
"shekaru 10 sun wuce bayan na yi ritaya, na ji an kara shirye-shirye daga rabin awa zuwa awa shida a kowace rana, lalle wannan babban ci gaba ne, kuma an gaya mana cewa, an kafa tashoshin FM a Yamai da bude shafinmu na internet, ga sabbin ma'aikata da yawa sun nuna himma da kwazo wajen aikinsu, sun zarce mu sosai, wannan ya faranta mana rai kwarai da gaske, ina fatan sashen Hausa zai ci gaba da samun bunkasuwa da ingantuwa, kuma ina fatan kada ku manta da mu tsoffin ma'aikata, wadanda suka taba sanya kokari cikin mawuyacin hali kafin ku zo sashenmu."
A'a, ko kadan ba za mu manta da su ba, kuma muna imanin da cewa, masu sauraronmu ma ba za su manta ba, sabo da su ne suka shimfida harsashi ga sashen Hausa na rediyon kasar Sin, kuma su ne suka shimfida harsashi ga gadar sada zumunta da fahimtar juna a tsakanin jama'ar Sin da na Afirka.
To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, amma kada ku manta, a makon gobe war haka, za mu ci gaba da kawo muku shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, "sai Allah ya kai mu ranar Jumma'a mai zuwa. (Lubabatu)
|