Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin, wata shahararriyar kungiya ce dake cike da kyakkyawan fata a sassan wasannin motsa jiki na kasar. A gun gasar wasannin Olympics da aka gudanar har sau shida a da, kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin, wata kungiyar wasa ce da ta fi samun lambobin zinariya a cikin kungiyar wakilai ta wasannin motsa jiki ta kasar Sin. A gun gasar wasannin Olympics ta Beijing da za a gudanar, ko shakka babu kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin za ta janyo hankulan mutane. Kwanakin baya dai, wannan kungiya ta yi horo na tsawon watanni hudu a fannin fasaha da inganta lafiyar jikuna musammman ma a fannin halin dan adam.
An raba horon cikin matakai biyu. Mataki na farko, an yi horo ne a birnin Beijing; Mataki na biyu kuma a birnin Jinan dake gabashin kasar Sin, inda kugiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin ta gudanar da gasar yini biyu ta zaben wadanda za su samu shiga wasannin Olympics. Mr. He Chong, dan wasan tsunduma cikin ruwa daga katato na tsawon mita uku ya fada wa wakilinmu cewa: " A duk tsawon lokacin yin hoton, 'yan wasan na kasarmu sun jurewa wahalhalu sosai yayin da ake gudanar da gasar zaben wadanda za su samu shiga wasannin Olympics. Da zarar muka kammala horon, sai nan da nan muka shiga gasar cin kofin duniya ta wasan tsunduma cikin ruwa, inda dukkan 'yan wasan suka yi fintinkau wajen gasar har suka samu sakamako mai tsoka sakamakon kyakkyawan ingancin horon da suka samu".
A matsayin wata kungiya mafi nagarta a duniya a fannin wasan tsunduma cikin ruwa, lallai 'yan wasa na kasar Sin suna kan gaba a fannin fasahohin da suke da su, wadanda kuma sukan yi horo na zaman yau da kullum daidai bisa tsarin da aka tsara.
Ko kuna sane da cewa, wasan tsunduma cikin ruwa, wani irin wasa ne dake bukatar samun kyakkyawan ingancin halin dan adam. Bisa zafafan gasanni na kasa da kasa, wassu 'yan wasa sukan sha kaye na ba zata sakamakon sauyin halin dan adam. Tare da la'akarin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008 da za a gudanar a nan birnin Beijing, mahukunta a kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin ta fi mayar da hankali kan horar da 'yan wasa a fannin halin dan adam. Mataimakiyar daraktan cibiyar kula da harkokin wasan iyo na kasa kuma kyaftin kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa takasar Madam Zhou Jihong ta bayyana cewa:" Yin horo a fannin halin dan adam na da muhimmancin gaske ga kowane dan wasa. Daga fannoni biyu ne ake yin horon. Fanni na farko shi ne dinga shiga gasanni don kyautata halin adan adam na 'yan wasa ; Fanni na biyu shi ne, samun karin ilmi a fannin halin dan adam lokacin da 'yan wasa suke samun horo ''.
Kwanan baya dai kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta kasar Sin ta gudanar da wata gasar bada lacca, inda 'yan wasa 15 suka tofa albarkacin bakinsu kan kyakkyawan burinsu na shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing. Wata 'yar wasa mai suna Wang Xin ta furta cewa : ' Lallai na ji tsoro sosai lokacin da nake yin lacca fiye da yadda nake yi lokacin da nake yin wasan tsunduma cikin ruwa daga katako'.(Sani Wang)
|