A ran 8 ga wata, an cimma nasarar mika wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma. Wannan shi ne karo na farko da aka kai wutar wasannin Olympic zuwa babban dutse mafi tsayi a duniya watau dutsen Qomolangma mai tsayin mita 8844.43. Kamfanin dillancin labaru na kasar Rasha Itar-tass da kamfanin dillancin labaru na Indo-Asian, da sauran muhimman kafofin yada labaru na duniya sun bayar da labarai kan wannan al'amari.
Kamfanin dillancin labaru na Indo-Asian ya bayar da labari cewa, mutane masu dauke da wuta 10 cikinsu har da 'yan kabilar Tibet 8, sun isa kololuwar Qomolangma, kuma a can ne, suka daga tutar kasar Sin da tutar wasannin Olympic na duniya da tutar wasannin Olympic na Beijing sama, kuma sun bayar da kayayyawan fata ga wasannin Olympic na Beijing kafin dukkan 'yan kallon na duniya.
"Yanar gizo ta Internet ta yada labaru ta Asia ta kasar Sinagapore" ta bayar da bayyanin edita cewa, yayin da matar da ke dauke da wuta ta kabilar Tibet Tsrenwangmo ta kasance dauke da wutar yola ta "Xiangyun" kuma ta tsaya a kan kololuwar duniya, ya bayyana mana cewa , bayan da aka mika wutar wasannin Olympic na Beijing har na tsawon lokaci, an cimma nasarar mika wutar wasannin Olympic na Beijing a kan babban dutse mafi tsayi a duniya. "Yanar gizo ta Internet ta hadaddiyar jaridar safe" ta bayyana cewa, mika wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma ya bayyana mana akidar wasannin Olympic na Beijing watau, shirya tsabtatacen wasannin Olympic mai al'adu da kuma kimiyya da fasaha.(Bako)
|