Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 10:48:50    
Bi da bi ne Mr. Hu Jintao ya gana da tsofaffin firaministaoci 4 na kasar Japan

cri

Ran 8 ga wata a hotel din da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka, ya ci abincin rana tare da tsofaffin firaministoci 4 na kasar Japan, wato Mr. Yasuhiro Nakasone, da Mr. Toshiki Kaifu, da Mr. Yoshiro Mori, da Mr. Shinzo Abe, an yi shawarwari mai aminci tare.

Mr. Hu Jintao ya yi nuni da cewa, yanzu habakar tattalin arzikin kasashen duniya tana ta bunkasuwa sosai, kuma ana kokarin sa kaimi ga habakar kasashen Asiya, kasashen Sin da Japan su ne muhimman kasashen duniya, yawan batutuwa da nauyin da suke fuskanta yana karuwa, kuma sun sami moriya iri daya da fannonin bunkasuwar tare ya fi yawa. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Japan domin cigaba da sada zumunci bisa manyan tsare tsare, da kuma karfafa hadin gwiwar da ke da moriyar juna, da fadada yin musanyar al'adu, da sa kaimi ga ayyukan raya nahiyar Asiya domin tinkarar kalublen kasashen duniya.

Mr. Yasuhiro Nakasone ya nuna cewa, takardu 4 da kasashen biyu suka daddale kan harkokin siyasa a wannan karo su ne kundin ja wa bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu gora.

Mr. Toshiki Kaifu ya ce, yana fatan kasashen biyu za su cigaba da kara yin musanya kan fannoni dabam daban, ta haka domin kara fahimtar juna da ke tsakanin kasashen biyu.

Mr. Yoshiro Mori ya yi bayani kan ra'ayinsa kan bunkasuwar kasashen Afirka, yana fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa domin ba da gudummawa tare ga bunkasuwar kasashen Afirka.

Mr. Shinzo Abe ya nuna cewa, ziyarce-ziyarcen da shugabannin kasashen biyu suka yi ga juna tana da muhimmiyar ma'ana wajen kyautata huldar da ke tsakanin kasashen biyu.