Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 21:40:46    
Wajibi ne, a dogara da jama'ar kasar Sin da Japan wajen yalwata sha'anin sada zumunta a tsakanin kasashen biyu, in ji Mr Hu Jintao

cri

Yau Alhamis, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bayyana a birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan cewa, ko ba dade ko ba jima, sada zumunta a tsakanin kasar Sin da Japan sada zumunta ce a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Jama'ar kasashen biyu tushe da ginshiki ne ga zumunta a tsakanin Sin da Japan, wajibi ne, a dogara da jama'ar kasashen biyu wajen yalwata sha'anin sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.

Mr Hu Jintao ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake halarci liyafar da kungiyoyin sada zumunta a tsakanin Japan da Sin guda 7 da kungiyoyin Sinawa hudu da ke zaune a kasar Japan suka shirya don yin maraba da shi. Ya kuma kara da cewa, sada zumunta a tsakanin Sin da Japan al'adar gargajiya ce ta tarihi, kuma tana dacewa da ci gaban zamani, kuma ya kamata, zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwa don moriyar juna, da kuma samun bunkasuwa tare manufa ce mai girma da kasashen biyu ke neman cim mawa tare.

Mr Hu Jintao ya ci gaba da cewa, yanzu, ana fuskantar sabuwar dama don kara yalwata hulda a tsakanin Sin da Japan. Yana jiran mutanen bangarori daban daban na kasashen biyu da su sa kaimi ga ciyar da sha'anin sada zumunta a tsakanin kasashen biyu gaba tare, don kawo zaman alheri ga jama'ar kasashen biyu da jama'ar Asiya da ta kasashe daban daban.

Bisa wani labarin daban da aka bayar, an ce, a wannan rana, a birnin Tokyo, bi da bi Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gana da Mr Kono Yohei, shugaban majalisar wakilai ta kasar Japan da Mr Eda Satsuki, shugaban majalisar datijai ta kasar.

A lokacin ganawar, Mr Hu Jintao ya nuna cewa, yalwata hulda a tsakanin Sin da Japan don moriyar juna kuma bisa manyan tsare-tsare yana dacewa da babbar moriyar kasashen biyu da jama'arsu, kuma yana kawo amfani ga tabbatar da zaman lafiya da zaman karko da wadata a Asiya da duniya.

A nasa bangare, Mr Kono Yohei ya bayyana cewa, ziyarar Hu Jintao ziyara ta farko ce da shugaban kasar Sin ke yi a kasar Japan a wannan karni. Yana fatan cikakkiyar nasara za ta tabbata ga ziyarar. (Halilu)