Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 21:05:43    
Kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun mai da hankula sosai kan kaiwa wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma

cri

A ran 8 ga wata, an cimma nasarar mika wutar gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing zuwa kololuwar Qomolangma. A farkon lokaci ne, kafofin watsa labaru na Jamus, da Australiya, da Korea ta kudu, da India, da Singapore da dai sauransu sun bayar da labarai kan haka.

Jaridar 'Suddentsche Zeitung' ta kasar Jamus ta bayar da wani bayani mai lakabi haka, 'kasar Sin ta mika wutar gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing a kolin duniya', inda aka gabatar da mambobin kungiyar hawan tsauni, da kuma yadda suke tafiya da mika wutar yola kan kololuwar Qomolangma.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Australiya wato ABC ta karfafa cewa, kungiyar hawan tsauni ta hada da mambobi 22 na kabilar Tibet, da wani 'dan kabilar Tujia, kungiyar hawan tsauni kuma ta hada da mata 3.

Ban da wannan kuma, kamfanonin dillancin labaru na Rusnes ta kasar Rasha, da tashar internet ta Lianhe zaobao ta kasar Singapore da dai sauransu sun mai da hankali sosai kan nasarar da kasar Sin ta samu wajen mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a kololuwar Qomolangma.(Danladi)