Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 20:15:52    
An mika fitilar wasannin Olympic na Beijing tare da nasara a birnin Shenzhen na kasar Sin

cri
Yau Alhamis, an mika fitilar wasannin Olympic na Beijing tare da nasara a birnin Shenzhen na lardin Guangdong da ke a kudancin kasar Sin.

Da ya ke yau da safe daidai lokacin da aka kai fitilar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma, an jirkita bikin fara mika fitilar a zangon Shenzhen daga karfe 8 na safe zuwa karfe 12 na tsakar rana. Bayan da masu mika fitilar da yawansu ya kai 208 suka bai wa juna fitilar, daga bisani an yi amfani da fitilar wajen kunna wutar tukunya da ke a filin yamma na cibiyar wasan motsa jiki ta birnin Shenzhen, ta haka an kammala aikin mika fitilar wasannin Olympic na Beijing a zangon Shenzhen tare da cikakkiyar nasara.

Dukan tsawon hanyar da aka bi wajen mika fitilar ya kai kilomita 41.6 a birnin Shenzhen. An ratsa da fitilar a wani wuri mai suna "tagogin duniya" da filin nuna hoton marigayi Deng Xiaoping da sauran muhimman gine-gine da shahararrun wurare na birnin, don nuna nasarorin da birnin ya samu wajen aiwatar da manufar gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a cikin shekaru 30 da suka wuce. (Halilu)