Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 19:53:47    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi muhimmin jawabi a jami'ar Wasedadaigaku ta Japan

cri
Yau a jami'ar Wasedadaigaku da ke birnin Tokyo na kasar Japan, shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya yi wani muhimmin jawabi, inda ya yi nuni da cewa, sada zumunta a tsakanin Sin da Japan harka daya ce ga jama'ar kasashen biyu, kuma matasa manyan gobe, karfafa huldar aminci a tsakanin kasashen biyu a nan gaba na dogara da su.

Jami'ar Wasedadaigaku na daya daga cikin mashahuran jami'o'in Japan, kuma ta kafu ne a shekarar 1882.

A cikin tafi mai yawa da ake yi, shugaba Hu Jintao ya fara muhimmin jawabi. Da farko, ya yi nuni da cewa,"Sin da Japan makwabta ne ga juna, kuma huldar da ke tsakaninsu na kan wani sabon mafari a tarihi. Da sahihin zuci ne, gwamnatin kasar Sin da jama'arta na fatan yin kokari tare da takwarorinsu na Japan, don kara amincewa da juna da karfafa dankon zumunci da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu, ta yadda za a kulla sabuwar huldar moriyar juna a tsakanin Sin da Japan."

A cikin jawabinsa, shugaba Hu Jintao ya kuma waiwayi manyan nasarorin da aka cimma wajen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen biyu a cikin shekaru 30 da suka wuce, ya kuma jaddada cewa, Sin ta bunkasa cikin sauri a cikin shekaru 30 da suka wuce ne sabo da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da ta yi, kuma dole ne Sin ta cigaba da aiwatar da manufar, don kara samun cigaba a nan gaba. Ban da wannan, ya kuma yi nuni da cewa, Sin za ta nace ga bin hanyar samun cigaba cikin lumana ba tare da sauyawa ba, ya ce,"Sin na tsayawa tsayin daka wajen bin manufar diplomasiyya ta zaman lafiya cikin dogara bisa karfin kanta, kuma tana nacewa ga bin manufar samun moriyar juna, tana kuma dukufa kan raya dimokuradiyya ga huldar da ke tsakanin kasa da kasa da ciyar da hadin kan tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata, da sa kaimi ga mu'amala a tsakanin wayin kai iri iri da raya duniya mai jituwa da ke da dadadden zaman lafiya da albarka. Sin na aiwatar da manufar tsaron kanta daga harin waje, kuma ba za ta shiga gasar ajiye makamai ba, haka kuma ba za ta zama barazanar soja ga kowace kasa ba, har abada ba za ta habaka kanta ba."

A cikin jawabinsa, Hu Jintao ya kuma gabatar da shawarwari game da bunkasa huldar moriyar juna a tsakanin Sin da Japan. Yana fatan Sin da Japan za su mayar da juna a matsayin abokiyar hadin gwiwa a maimakon dan takara ga juna, su nuna goyon baya ga bunkasuwar juna cikin lumana, su dauki cigaban juna a matsayin zarafi a maimakon barazana, su girmama moriyar juna da kuma daidaita sabani ta hanyar shawarwari.

Bayan haka, Hu Jintao ya jaddada cewa, sada zumunta a tsakanin Sin da Japan harka daya ce ga jama'ar kasashen biyu, wanda ke bukatar kokarin jama'ar kasashen biyu baki daya, ya kuma yi kira ga matasan kasashen biyu da su ba da taimakonsu."Matasa manyan gobe, kuma makomar huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Japan na dogara ne a gare ku. Na taba shafe shekaru da dama ina kulawa da harkokin matasa, sabo da haka, ina son kasancewa tare da matasa, domin kuruciyarsu. 'shekaru na iya canza fuskar jama'a, amma ba za su iya sauya abokantakar da ke tsakaninsu ba.' Tarihi ya gaya mini, zumuncin da aka kulla a lokacin matasa, zai raka mu har iyakacin rayuwarmu. Ya kamata mu yi kokari tare, don yada zumuncin da ke tsakanin Sin da Japan."(Lubabatu)