Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 17:32:44    
Fatima Mehmood, wata lauya daga kabilar Ozbek

cri

Fatima Mehmood, 'yar kabilar Ozbek daga jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Ta taba kafa kamfanin lauya na kananan kabilu na farko a nan kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan Fatima Mehmood.

Fatima Mehmood ta fito ne daga birnin Tacheng da ke arewacin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta. A wannan birnin da ke da tsawon kilomita fiye da goma da tashar shigi da fici a tsakanin kasashen Sin da Kazakhstan, akwai kananan kabilu da yawansu ya kai guda 29 suna zama a nan, ciki har da kabilun Ozbek, da Uygur, da Tatar, da Rasha, da Daur, da dai sauransu. Iyalin Fatima 'yan kasuwa ne daga zuriya zuwa zuriya, amma Fatima ta zama lauya mata ta farko daga kabilarsu. Wannan na da nasaba kai tsaye da wani filim na kasar India mai suna "Awara". Fatima ta ce,

"A cikin wannan filim, kariyar da lauya ta bayar, ta canja zaman rayuwar mutane sosai, lallai filim ya burge ni sosai. Daga baya kuma, a lokacin da nake zaben sana'o'i, sai na zabi zaman wata lauya."

A shekarar 1985, bayan da Fatima ta gama karatunta a sashen ilmin shari'a na jami'ar jihar Xinjiang, sai ta koma garinta na Tacheng, kuma ta soma aikin sana'ar lauya a wani kamfanin lauya kan harkokin tattalin arziki da gwamnatin wurin ta kafa.

Ta shari'a ta farko da ta karba, ta gane ma'anar aikinta. Wancan ce wata shari'ar dabaibaye kan gajyar dukiyoyi. 'Yan uwa na Kuknyva, wata mace ta kabilar Rasha, sun kwace ikonta na gaji dukiyoyi, saboda haka Kuknyava ta neman taimako daga Fatima. Bisa isasshen shaidu, Fatima ta samu nasara wajen shari'ar. Fatima ta waiwayo cewa,

"A lokacin, na shiga zaman al'umma ba da dadewa ba, a gani na, sai dai na yi amfani da ilmomin shari'a da na koya, don kare halatacen ikonta kawai, amma wannan ne muhimmin abu ga Kuknyva a duk rayuwarta. Ta yadda na gane, lallai sana'ar lauya tana da muhimmanci sosai."

Saboda ta kware a sana'ar lauya, kuma tana iya harsuna na kananan kabilu da yawa, don haka, kullum Fatima na iya karbar shri'o'i da dama. Amma, a shekarar 1995, a karkashin tasirin da halin da ake ciki a lokacin ke kawo mata, Fatima ta soma aikin ciniki. Amma, maganar da babanta ya gaya mata, ta sanya Fatima sake koma sana'ar lauya.

"A lokacin, babana ya gaya mini cewa, ''yan kasuwa masu arziki na kabilarmu ta Ozbek suna da yawa, amma ke ce lauya daya kawai daga kabilar Ozbek daga zuriya zuwa zuriya. Ya kamata ki yi aikin sana'ar lauya, kuma zaman al'umma na bukatarki.' Bayan da na ji maganar babana, sai na canja ra'ayina."

Tun shekaru fiye da goma da suka wuce, Fatima ta gudanar da shari'o'i na keta dokoki, da na doka ta tanadar, da na tattalin arziki, da kuma na kasashen ketare, wadanda yawansu ya kai kusan dubu goma, kuma tana dare kujerar mai ba da shawara kan shari'a ta kamfanoni sama da 50.

A matsayinta na wata lauya daga kananan kabilu, Fatima ta fi mayar da hankali kan mutane marasa karfi, Fatima da lauyuka na kamfaninta su kan ba da shawara na kyauta ga mutanen da suka fi fama da talauci, da nakasassu. Ta ce,

"Lallai, mutane marasa karfi, ciki har da mutanen da ke bisa matsayin zaman rayuwa mafi kankanta, suna fama da talauci sosai. Saboda haka, muna bayar musu da shawara a fannin shari'a ba tare da bisa kudi ba. Mu ma muna yin haka ne ga 'yan iyalai na 'ya'yan Sinawa mazauna kasashen ketare."

A watan Feburairu na shekarar 2006, birnin Tacheng ya kafa "tashar ayyukan kiyaye ikon mata da na yara", da kuma "Tashar shari'a ta ayyukan 'yan iyalai na 'ya'yan Sinawa mazauna kasashen ketare" a kamfanin lauya na Fatima. Haka kuma, mutanen da ke neman kariya daga Fatima suna ta kara yawa. A hakika dai, domin gabatar da hidima mai kyau a fannin shari'a, kullum Fatima na kulawa da horar da lauyuka matasa masu kwarewa, a lokacin da take gabatar musu damar samun aikin yi, a waje daya kuma, ta kan bayar musu fasahohin da ta samu wajen ayyukan ba da kariya.

Ko da ya ke Fatima ta samu sakamako sosai, amma a matsayinta na wata lauya mace daga kananan kabilu, ta kan gamu da rashin fahimta daga wasu mutane. Amma, sadaukar da aikinta da Fatima ke yi, ta burge da kawo tasiri ga kowa da kowa da ke kewayenta. Wang Chaoyang, wani lauya da ke aiki a kamfaninta ya ce, "A farko, Fatima ta kan gamu da rashi fahimta kan aikinta. Amma, tana ganin cewa, aikin lauya na da amfani ga farar hula, saboda haka, kullum tana tsayawa kan aikinta. Yanzu, mutane suna ta kara fahimtar aikin da ta zaba. Mu abokan aikinta na maza muna girmama mata sosai."

A ziyara ta karshe, Fatima ta gaya wa wakilinmu cewa, akwai doguwar hanya nan gaba, za ta yi iyakacin kokarinta don bayar da hidima ga 'yan uwansu daga yankunan kananan kabilu.(Bilkisu)