Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 17:02:45    
Kasar Sin za ta kara gudanar da ayyukan share fage na muhimmin wa'adi na gasar wasannin Olympics da kyau, in ji Mr. Xi Jinping

cri

A ran 7 ga wata a birnin Qingdao, a gun taron ayyukan share fage ga gasar wasannin Olympic da za a shirya a sauran wurare ba birnin Beijing ba, mataimakin shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya jaddada cewa, ayyukan share fage na gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, da kuma gasar Olympics ta nakasassu sun shiga cikin wani mihimmin wa'adi, kamata ya yi birane daban daban da za su taimakawa shirya gasannin su kara yin kokari, domin aiwatar da ayyukan share fage na muhimmin wa'adi na gasar wasannin Olympics da kyau.

Mr. Xi ya ce, a halin yanzu dai, ana gudanar da ayyukan share fage na gasar wasannin Olympics kamar yadda ya kamata, ta hakan ne, an sanya wani tushe mai inganci da za a shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu da kyau kuma da ke da sigar musamman. Kamata ya yi birane daban daban da za su taimakwa shirya gasannin su kara sa kaimi wajen tafiyar da ayyukan share fage na muhimmin wa'adi, domin cimma burin shirya filaye da dakuna, da fasahohi da kyau, da tafiyar da harkokin tsaro da ba da hidima ga manema labaru yadda ya kamata, da kuma gudanar da harkokin biranen da ba da tabbaci cikin ruwan sanyi.(Danladi)