Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 16:54:40    
Mr Hu Jintao ya bayar da jawabi mai muhimmanci a Jami'ar Wasedadaigaku ta kasar Japan

cri
Ran 8 ga wata, Mr Hu Jintao, shugaban kaasar Sin ya bayar da jawabi mai muhimmanci a Jami'ar Wasedadaigaku da ke a birnin Kyoto na kasar Japan. A cikin jawabinsa, ya nuna cewa, dankon zumunci a tsakanin kasar Sin da Japan sha'ani ne bai daya ga jama'ar kasashen biyu. Samarin kasashen biyu sabon karfi ne mai muhimmanci ga dankon zumunci a tsakanin Sin da Japan, makomar dankon aminci a tsakanin kasashen biyu za ta dogara da samari sosai.

Bisa halin da ake ciki a yanzu da tarihi, Mr Hu Jintao ya bayyana hanyar da kasar Sin ta bi wajen samun bunkasuwa. Ya waiwayi hanyar da kasar Sin ta bi wajen yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa da kuma manyan nasarorin da ta samu a cikin shekaru 30 da suka wuce. Bayan haka ya nuna cewa, ko da yaushe kasar Sin tana bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana. Wannan zabe ne da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka yi bisa manyan tsare-tsare. Ya nanata cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufar tsaron kai game da harkokin tsaron kasa, ba ta yin gasar makamai, ba ta yin barnaza ga dukan kasashe a fannin aikin soja, kuma ba za ta bi akidar nuna isa da neman habaka ba har abada.

Mr Hu Jintao ya ci gaba da cewa, tarihi kyakkyawan littafin koyarwa ne na filosofiya. An jaddada tunawa da tarhi ba don kara nuna kyama ba, bamban da haka don tsamo darasi daga tarihi ta yadda za a fuskanci nan gaba da kishin zaman alfiya da kiyaye shi, A bar jama'ar kasar Sin da Japan su yi abuta da juna daga zuriya zuwa zuriya, a bar jama'ar kasashe daban daban su more zaman lafiya har abada. (Halilu)