Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 16:01:44    
Gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta kasance gasar wasannin Olympics da za'a fi yin amfani da kimiyya da fasaha, in ji ministan kimiyya da fasaha na Sin

cri
Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang ya bayyana yau 8 ga wata a nan birnin Beijing cewar, gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta kasance gasar wasannin Olympics da za'a fi yin amfani da kimiyya da fasaha a cikin tarihi.

A wajen taron manema labaru da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a wannan rana, Wan Gang ya ce, tun daga birnin Beijing ya cimma nasarar samun damar daukar bakuncin gasar wasannin Olympics shekaru 7 da suka gabata, kasar Sin ta haye wahalhalu da dama da yin amfani da fasahohin zamani daban-daban yayin da take zage damtse wajen shirya gasar wasannin Olympics, wato tana kokarin biyan bukatun gasar wasannin Olympics a fannin kimiyya da fasaha, ciki har da gina dakuna da filaye na wasannin Olympics, da shirya gagarumin biki, da shirya gasanni yadda ya kamata. A waje daya kuma, domin cimma burin shirya wata gagarumar gasar wasannin Olympics ba tare da bata muhalli ba, da yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli, kasar Sin ita ma ta kaddamar da ayyukan raya fasahohin gina kyawawan gine-gine, da raya makamashi mai tsabta, da kiyaye muhallin halittu da dai sauransu.(Murtala)