Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 15:43:13    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Wani dalibi yana neman bayanin da ya rubuta domin samun digirin Phd. Wani dablibin dake nazarin ilimin filosiya yana nan neman wani bayanin da ya rubuta bayan da aka yi wa gidansa sata, dalili kuwa shi ne ya rubuta bayanin nan da inji mai kwakwala ya kuma adana shi a cikin komputer.da barawo ya yi wa gidansa sata,ya kwashi injin da kudin Sin sama da Yuan dubu bakwai tare da sauran kayayyaki masu daraja na gida. Da ganin haka wannan dalibi ya rubuta wasika zuwa ga wata jarida inda ya yi fatan barawo ya aika masa bayanin da ya tanada a cikin injin wanda yake da muhimmanci sosai wajen neman samun digirin PhD.

Wani matashi ya kwace wata budurwa. Kwanan baya an tsare wani matashi sabo da ya kwace masoyiyarsa a yankin musamman na tattalin arziki na Shezhen dake kudancin kasar Sin. Suna matashi shi ne Zhang ya fara soyayya da budurwa Peng a watan Satumba da ya gabata. Ya yi gayyar kokarin yin zambar kudinta da ya san ta da kudi mai yawa.duk da haka bai cimma ruwa ba. Sai ya yi shirin fashin budurwar tare da taimakon abokansa Li da Wang. A ran 21 ga watan Nuwamba na shekarar bara,wannan matashi mai suna Zhang ya cuci masoyiyarsa da cewa wani bakon dake cikin hotel yana da wani abu mai daraja yana so ya sayar da shi,yana fatan masoyiyarta ta je hotel domin saye shi. Da masoyiyarsa ta shiga hotel din da wuya, sai matasa uku sun yi mata fashi,sun kwace kudin dake cikin aljihunta na kudin Sin Yuan dubu sha daya da dari tara.Daga baya 'yan sanda sun tsare su gaba daya.

An shafe shekaru shida wajen jigilar dutse mai daraja. Wani babban dutse mai daraja da ake kiran Hetian jade ya isa yankin musamman na tattalin arziki na Shenzhen bayan an shafe shekaru shida an yi jigilarsa. Nauyin dutsen ya kai Ton 11, tsawonsa ya kai mita 3.75 da tsayinsa ya kai mita 1.35 da kuma fadinsa ya kai mita 1.44. malami Deng Jianxin dake zama a Shenzhen ya saye wannan dutse mai daraja nan da shekaru shida da suka shige a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta.dutsen nan yana cikin duwatsun Kunlun. A cikin shekarun shida da suka gabata a ko wane lokacin kankara aka tura dutsen nan mai daraja daga sama zuwa kasa a kai a kai,dabaya dutsen ya isa gefen babbar hanyar mota bayan da ya yi tafiya mai nisa kilomita dari biyar. A makon jiya dutsen mai daraja ya isa yankin Shenzhen. Kudin jigilarsa ya kai kudin Sin Yuan dubu talatin wato dalar Amurka 4200. kwararru masana ilimin duwatsu masu daraja suna sa ran cewa darajar dutsen y kai kudin Sin Yuan miliyan sittin.

Yana kokarin mayar da kudi ga mai shi. Wani mutum mai suna Chen ya gano kudin Sin Yuan dubu daya da dari biyar da wani katin banki a kan wani injin kudi na ATM a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, ya yi sama da wata daya yana jiran a mayar da kudin da kayan ga mai shi. Malami Chen mai gadi ne a bank, ya ce banki na ta kokarin neman samo wanda ya bace kudinsa amma ya gaza. Malami Chen ya ce idan mai batar kudin bai zo ba cikin 'yan kwanaki masu zuwa, zai mayar da kudin ga kungiyar taimakon yara kanana.(Ali)