Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 15:41:27    
Ra'ayin Mr Photisaro na kasar Thailand dangane da birnin Guangzho na kasar Sin

cri

Za mu kai ziyarar ban girma ga Mr Photisaro wanda shi ne dan Diplomasiya na kasar Thailand. Shi karamin jakada ne na karamin ofishin jakadanci na kasar Thailand a birnin Guangzhou na kasar Sin. Kafin ya zo nan kasar Sin shi jakadan kasar Thailand a kasar Kampuchea. Da ya ke ya yi aiki a kasar Sin da bai kai shekara guda ba, yana kaunar wannan kyakkyawan birni Guangzhou na kasar Sin.

A wata rana da yamma a karshen watan Disamba na shekarar bara, bisa gayyatar da aka yi masa,wakilin gidan rediyonmu ya shiga bene na biyu na Huayuan Hotel dake birnin Guangzhou?inda karamin ofishin jakadanci na kasar Thailand a birnin Guangzhou na kasar Sin yake. Mr Photisaro ya gana da wakilin gidan rediyonmu tare da fara'a jin kadan bayan da ya kammala wani taro. Shi dattijo ne mai kamili, gashinsa fari ne da dan toka, cikin kayan mai launin toka na kasashen yammma da jan taye a wuya da tabarau babba.

Birnin Guangzhou, babban birni ne na lardin Guangdong na kasar Sin wanda ya yi karfi wajen tattalin arziki, kasuwanci ya fi bunkasa a wannan wurin. Wannan abu ya burge Mr Photisaro wanda zamansa a birnin bai kai shekara guda ba. A ganinsa kasuwanci na birnin Guangzhou ya yi daidai da na sauran birane na duniya.

"Mutanen da ke zama a birnin Guangzhou suna aiki kamar agogo ba tsayawa dare da rana,ko ina ka sa kafa ka iya tarar da 'yan kasuwa, suna maganganu tattare da ciniki ko odar kayayyaki ko kuwa sayar da kayayyaki. Ga manyan gine ginen ciniki masu benaye da dama a tsaye suke a gefunan biyu na tituna,ga hajoji iri iri daga alatu zuwa sauran kayan gida,kome kana so ka iya same su a kasuwannin birnin Guangzhou."

Mr Photisaro ya bayyana cewa ba nisa sosai tsakanin lardin Guangdong na kasar Sin da kasar Thailand, shi ya sa da akwai mu'amalar ciniki dake kasancewa tsakaninsu kullum,lardin Guangdong muhimmiyar kawar ciniki ta kasar Thailand. Yana mai ra'ayin cewa saurin ci gaban tattalin arzikin lardin Guangdong na kasar Sin ya ja tattalin arziki da ciniki na kasar Thailand gaba a fili.

"lardin Guangdong na kasar Sin ya kusanci kasar Thailand, mutanen kasar Thailand masu jinin mutanen Sin da yawa sun isa kasar Thailand ne daga birane Xiantou da Chaozhou na lardin Guangdong da gundumar Wenchang ta lardin Hainan. Idan aka kwatanta lardin Guangdong da sauran larduna na kasar Sin, lardin Guangdong ya fi su yawa wajen yin mu'amalar tattalin arziki da ciniki da kasar Thailand."

Bayan da ya sauka a lardin Guangdong na kasar Sin, Mr Photisaro ya kai ziyara a birane na Shenzhen da Dongguan, ya yi farin ciki sosai da ganin ci gaban da aka samu wajen shimfida masana'antu da sana'o'in kimiyya da fasahohi na zamani a wadannnan birane. Da wuya a amince da cewa wadannan wurare kauyuka ne a da. lardin Guangdong ya samu cikakkiyar nasara wajen karkata alkiblarta daga salon tattalin arziki bisa shiri zuwa salon tattalin arziki na kasuwanci. Da akwai abubuwa da dama da suka isa abun koyo ga kasar Thailand. A ganin Mr Photisaro yana da hakkin gabatar da fasahohin da lardin Guangdong ya samu ga kasar Thailand da bayar da taimakonsa ga ci gaban tattalin arziki na kasar Thailand.

Ban da fasahohin bunkasa tattalin arziki, da akwai wani abu daban na lardin Guangdong da Mr Photisaro yana fatan ya gabatar da shi zuwa mutanen kasar Thailand shi ne abinci mai dadi. Abincin lardin Guangdong ana kiransa abincin Yue cikin harshen sinanci, yana daya daga cikin manyan tsare tsare hudu na abincin kasar Sin wanda ya fi shahara kan yawan abubuwan masu ban mamakin da ake amfani da su wajen dafa abinci. Mr Photisaro ya ce yayin da yake a kasar Thailand, ya kan je dakunan sayar da abincin Sinawa, ya fi son cin abincin Yue.

Ya ce " babu banbance banbance masu yawa tsakanin abincin sinawa da abincin Yue. Mutanen kasar Sin da suka zo daga biranen Chaozhou da Xiantou sun bude dakunan sayar da abincin sinawa da yawa a kasr Thailand. Yayin da na ke Thailand, na kan je wadannan wadannan wuraren. Bayan isowarta a birnin Guangzhou, karo na farko ne na dandana ainihin abincin Yue,ya burge ni sosai har yanzu ba zan iya mantar da shi ba. Wani abu da na fi so a birnin Guangzhou shi ne karya kumallo. Abincin da mutanen Guangdong suke ci a lokacin karya kumallo ina so in gabatar da shi ga mutanen Thailand, na tabbata za su iya kaunar shi."

A karshen mako, Mr Photisaro da matarsa da kuma 'ya'yansu su kan dandana ire iren abinci masu dadi na lardin Guangdong. Ya ce raka matata cin abinci da sayaya abubuwan nishadi gare ni a birnin Guangzhou.

"Mutanen da suka sauka a birnin Guangzhou su kan je shagunan dake bakin titin Shanxi domin saye tufafi, masu yawon bude idanu su kan je shagunan dake bakin titin Beijing domin saye abubuwan tunaniya, a shagunan dake bakin titin Yide su saye kyaututtuka, a kasuwar Haiyin su saye kayayyakin gida masu amfani da wutar lantarki da kayayyakin zamani na digital. Abun da ya fi ba ni sha'awa wajen yin saye saye a birnin Guangzhou shi ne za ka yi tayi yadda ka ga dama."

Da ya dade a birnin Guangzhou, Mr Photisaro ya fara nuna sha'awarsa al'adun Guangdong. Ya fara sauraron kade kade na Hongkong da na Taiwan da kallon wasannin Opera na lardin Guangdong, ya kuma tattara kayayyakin tangaram.

Wata rana gwamnatin birnin Foshan na lardin Guangdong ta gayyaci kanana jakadu na kasashen waje a birnin Guangzhou da su kai ziyara a wani tsohon murhu dake yankin Foshan wanda yake da tarihi na shekaru dari biyar, inda aka yin tangaram har wa yau dai ya kasance kamar yadda yake a can zamanin da, kuma murhu ne da ya fi dadewa a duniya. Da Mr Photisaro ya ga tangaram da aka samu daga wannan murhu, wannan tsohon kayan fasaha ya dauke hankalinsa nan take. Daga nan Mr Photisaro ya kan tafi masana'atar kera kayayyakin fasaha na tangaram da babban dakin adana kayayyakin tarihi na tangaram na birnin Foshan, ya kuma fara tattara kayayyakin tangaram. Ya ce,

"Na tattara abubuwan da dama da suka shaida abin da mutanen kasar Sin ke so kamar su samun sa'a da albashi mai tsoka da kuma tsawon rai, da kuma wani mutum mutumin jarumin kasar Sin Guan Gong da da kayayyakin fasaha na tangaram daban daban. Kayayyakin fasaha na tangaram na Foshan suna da kyaun gani, kuma ba su da tsada, tattara kayan tangaram ya zama wabun da nake so in yi bayan da na isa birnin Guangzhou na kasar Sin."

Abubuwan da Mr Photisara ya tattara sun yi yawa, har ma ya zama gwani a fannin nan. Yanzu ya san abin da aka zana kan jikin kayan tangaram ke nufi. Kamar su ya san wani irin 'ya'yan itatuwa da ake kira "peach" a turance alamu ne na samun tsaron rai. Sifoffin dragon da phoenix da crane,alamu ne na nuna aminci da fatan alheri. Bishiyoyi da furanni iri iri da aka zana a jikin kayan tangaram sun bayyana nagartattun halayen da mutanen kasar Sin suke so su mallaka.

Mr Photisaro ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa ko da ya ke zamansa a kasar Sin bai cika shekara guda ba, hankalinsa ya dade yana kan al'amuran kasar Sin, dalili kuwa shi ne kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya, mutanen kasar Thailand sun kara mai da hankulansu kan kasar Sin. Ya ce,

"A cikin shekarun baya kafofin yada labarai na kasar Thailand sun kara mayar da hankulansu kan kasar Sin da juyin da ake yi a kasar Sin, sabili da juyi a kasar Sin ya kawo tasiri ga duniya ciki har da Thailand."

Mr Photisaro ya ce a da kafofin yada labarai na kasar Thailand sun bayar da labarai dangane da kasar Sin bisa labaran da suka tsamo daga kamfanonin dillancin labarai na kamfanin Associated press na Amurka da kamfanin Reuter da kuma na kasar Faransa. Ga shi a yau kamfanonin kasar Thailand sun bayar da labarai dalla dalla dangane da kasar Sin. Wasu kamfanonin yada labarai na kasar Thailand sun daukar 'yan jarida da suka fahimci harshen sinanci duk domin samar da labarai cikakku da na gaskiya.

Mr Photisaro ya ce"na ba ku wani misali,kamfanin yada labarai na jaridar Manager daily na kasar Thailand yana da wasu 'yan jarida masu jin harshen sinanci, sun dau nauyin nazari da fassara labarai na kasar Sin da kuma bude shafi na musamman dangane da kasar Sin."

Babbar matsala da Mr Photisaro yake fama da ita yayin da ya sauka a kasar Sin ita ce harshe.A ganinsa idan kana so ka san al'amurn kasar Sin, sai ka yi mu'amala da mutanen Sin da kulla aminci da su,idan ba ka jin harshensu da wuyan ka yi mu'amala da su. Bisa yunkurin da ya yi, a watan Augusta na shekarar bara karamin ofishin jakadanci na kasar Thailand a birnin Guangzhou da jami'ar koyon harsunan waje na tattalin arziki da ciniki ta birnin Guangzhou a hade sun gayyaci malaman koyarwa na manyan makarantu na Sin da Thailan kimanin dari sun yi tattaunawa kan koyar da harshen sinanci da na Thailand. Ya kuma kawo shawara ga daliban Thailand da su dauki harshen sinanci a matsayin harshen da ya kamata su koyi.(Ali)