Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 15:00:45    
Hadaddiyar sanarwa kan raya dangantakar cimma moriyar juna bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Japan

cri

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda a yanzu haka yake ziyara kasar Japan, da firaministan Japan Fukuda Yasuo sun rattaba hannu kan "Hadaddiyar sanarwa kan daukaka cigaban dangantakar cimma moriyar juna bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Japan" jiya 7 ga wata a babban birnin Japan wato Tokyo. Sanarwar ta kasance takardar bayani ta siyasa ta hudu da aka daddale tsakanin kasashen biyu wato Sin da Japan.

Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya cewar, dangantakar dake kasancewa tsakanin Sin da Japan, tana daya daga cikin dangantakar bangarori biyu mafi muhimmanci gare su, zaman lumana cikin dogon lokaci da yin hadin-gwiwa da dankon zumunci, zabi ne kawai ga kasashen biyu. Bangarorin biyu sun yanke shawarar daukaka cigaban huldar cimma moriyar juna bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni a tsakaninsu, domin cimma burin kasancewar Sin da Japan tare cikin lumana, da dankon aminci zuriya bayan zuriya, da yin hadin-gwiwa da cimma moriyar juna, da kuma neman bunkasuwa cikin hadin-gwiwa.

Bangarorin biyu sun tabbatar da cewar, kasashen Sin da Japan, aminan hadin-gwiwa ne, ba za su kawowa juna barazana ba. Bangarorin biyu sun sake nanata cewar, za su nunawa juna cikakken goyon-baya wajen neman bunkasuwa kafada da kafada, da tsayawa tsayin daka kan daidaita matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari da tattaunawa.

Bangaren Japan ya sake jaddada matsayin da yake tsayawa a kai dangane da batun Taiwan, kamar yadda yake bayyana a hadaddiyar sanarwa tsakanin Japan da Sin.

Jiya da maraice, shugaba Hu Jintao ya gana da shugabannin manyan jam'iyyun siyasa na kasar Japan a birnin Tokyo daya bayan daya, ciki har da jam'iyyar 'yanci da dimokuradiyya, da jam'iyyar New Komeito, da jam'iyyar dimokuradiyya, da jam'iyyar kwaminis, da jam'iyyar Social Democratic. Shugaba Hu ya yi nuni da cewar, hadaddiyar sanarwa kan daukaka cigaban dangantakar cimma moriyar juna bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni da aka daddale tsakanin Sin da Japan, za ta zama jagora mai muhimmancin gaske ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu.(Murtala)