Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 16:52:45    
(Sabunta1)An cimma nasarar kai wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma

cri

Ran 8 ga wata, an cimma nasarar mika wutar gasar wasanin motsa jiki ta Olympic ta Beijing zuwa kololuwar Qomolangma, wannan shi ne karo na farko da aka kaiwa wutar wasannin Olympic zuwa Qomolangma watau babban dutse mafi tsayi a duniya, wanda tsawonsa ya kai mita 8844.43 a cikin tarihin gasar wasannin Olympic ta duniya.

A gun bikin "mika wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma" da aka yi a wannan ranar, da karfe 3 da sanyin safiya, jogora 12 na mambobin hawan dutse sun fara hawan kololuwar Qomolangma daga sansaninsu da ke mita 8300. Da karfe 9 da mintin 10 na safe agogon Beijing, mutum mai hawan dutse, Ivorbuzhadu ya kama fitilar, bayan da Jiji da Wang Yongfeng da Nimaciren da Huang Chungui suka mika wutar, da karfe 9 da minti 18 da safe agogon Beijing, a karshe, an mika wutar yola zuwa Tsrenwangmo, kuma an cimma burin mika wuta a dutsen Qomolangma. Tutar kwamitin wasannin Olympic na duniya da tutar kasar Sin da tutar gasar wasannin Olympic ta Beijing suna karkatawa cikin iska a kololuwar Qomolangma.

Bayan da aka cimma nasarar mika wutar wasannin Olympic na Beijing a dutsen Qomolangma, ran 8 ga wata, mataimakin shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga kungiyar hawan dutse Qomolangma ta mika wutar wasannin Olympic ta Beijing. A cikin sakon, an bayyana cewa, wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta ci bal-bal a dutsen Qomolangma, ya nuna mana cewa aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a dutsen Qomolangma ya sami cikakkiyar nasara. Wannan shi ne abin al'ajabi a cikin tarihin wasannin Olympic na duniya, kuma shi ne wani abin kyauta da jama'ar Sin suka baiwa gasar wasannin motsa jiki ta Olympic da kuma dukkan dan Adam tare.(Bako)