Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 11:20:43    
Ziyarar da aka yi a garin Soweto "wuri mai tsarki na juyin juya hali" na kasar Afirta ta kudu

cri

Garin Soweto da ke kudu maso yammacin Johannesburg birni mafi girma na kasar Afirta ta kudu shi ne wani mashahurin garin al'ummar bakakken fata na kasar Afirka ta kudu, kuma shi ne inda aka fara yin fama da darikar wariyar launin fata, a Soweto, ko ina ana iya samun tarihin yin fama da mulkin mallakar mutanen farar fata ta darikar wariyar launin fata da mutanen bakakken fata na kasar suka yi, garin Soweto shi ne wani "wuri mai tsarki na juyin juya hali" da ke zukatan mutanen bakakken fata na kasar Afirta ta kudu.

A kwanakin baya, manema labaru na kamfanin dilancin labaru na Xinhua sun shiga dakin adana kayan tarihin gwagwarmaya da wariyar launin fata da ke garin Soweto. Mr. Denny Schmitt ja gora na wannan dakin adana kayan tarihi ya taba shiga ayyukan neman 'yancin al'ummar bakakken fata sau da dama, bayaninsa da kayan tarihi sun fahimtar da mana tarihin ayyukan yin fama da darikar wariyar launin fata da aka yi.

A ran 16 ga watan Yuni na shekarar 1976, 'yan makaranta bakar fata kusan dubu 20 da ke garin Soweto sun yi zanga-zanga domin nuna adawa da a aiwatar da tsarin yin amfani da harshen Afrikander a makaranta na mutanen bakakken fata da karfi. wannan ya sami kisan gilla mai tsanani, an kashe 'yan makaranta da yara fiye da 500, wannan ya haddasa "batun Soweto" wanda ya firgitar da kasashen duniya sosai. Daga baya, da sauri ne fama ya yadu a yawancin wuraren kasar, gwamntin kasar ta aika da sojojin 'yan sanda fiye da dubu daya domin yin kisan gilla, wannan ya sake haddasa mutuwar 176, sauran mutane 1228 sun jikkata, kuma an kama mutane da yawa wadandaba su ji ba su gani ba.

"Aikin Soweto" da ya faru a shekarar 1976 ya canja tarihin kasar Afirka ta kudu. Bayan haka, ana yi ta bukatar a saki fursunonin da ke daukar ra'ayoyin adawa kan harkokin siyasa, da soke dokar hana kafa kungyar siyasa, da kuma kafa tsarin mulkin dimokuradiyya har zuwa a soke akidar wariyar launin fata a karshe. Bayan kafuwar sabuwar kasar Afirta ta kudu a shekarar 1994, gwamnatin kasar Afirka ta mayar da ran 16 ga watan Yuni ya zama ranar matasa a ko wace shekara domin tunawa da mutanen da suka rasu saboda yin adawa da akidar wariyar launin fata.

A cikin dogon lokacin yin fama da darikar wariyar launin fata, Soweto ya haifar da shugabannin bakakken fata wadanda suka kirkira tarihi, ciki har da Mr. Nelson Mandela tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu da marigayi Walter Sisulu tsohon mataimakin shugaban majalisar jama'ar kasar.

Yanzu a garin Soweto, ana iya ganin jerin kyakkyawan gidanen kwana, wannan unguwar mutane masu kudi. Amma, muna iya ganin unguwannin talakawa masu yawa, ya zuwa yanzu, akwai mutanen bakakken fata suna zama cikin talauci sosai. Bayan an soke tsarin akidar wariyar launin fata, aikin mafi muhimmanci ga gwamnatin kasar Afirta ta kudu shi ne warware matsalar talauci ga mutanen bakakken fata.

Ban da matsalar talauci, a cikin dogn lokacin da suka gabata, an sami batutuwan laifuffuka masu yawa a garin Soweto, amma gwamnatin ba ta "manta da shi" ba, ta bayar da manufofi a jere bisa saukakan sharudda domin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da manyan gine-gine da ke wurin.

Garin Soweto yana da talauci da albarka. Yana da dogon tarihi da salon zamani. Yana da bakin ciki a tarihi da kuzari a yanzu. Wannan kuzari yana nunawa da cigaba da makomar sabuwar kasar Afirta ta kudu.