Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 10:54:03    
Idan rukunin mabiya Dalai Lama na goyon-bayan raya wata zamantakewar al'umma mai jituwa, ya kamata su daina rura wutar tashin-hankali, a cewar Jaridar People'Daily

cri
Jaridar People's Daily ta kasar Sin da aka wallafa yau 8 ga wata ta bayar da wani bayani, inda ta bayyana cewar, idan rukunin mabiya Dalai Lama na goyon-bayan raya wata zamantakewar al'umma mai jituwa, to, kamata ya yi su daina duk wani yunkurin kulla makarkashiyar rura wutar tashin-hankali ba tare da bata lokaci ba.

Bayanin ya ce, ko a da ko a yanzu, al'ummar kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan raya wata zamantakewar al'umma mai jituwa. Kwanan baya, rukunin Dalai Lama "wadanda suka bayyana fatansu na zama memba na Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin" sun fito fili sun nuna amincewa da goyon-baya ga ra'ayin zaman jituwa.

Amma, rukunin mabiya Dalai Lama sun kulla makarkarshiyar rura wutar tashe-tashen hankula a ranar 14 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, sun yi zagon-kasa ga zaman lafiyar al'ummar Tibet, da kawo fargaba da bala'i ga wadanda ba su ci ba su sha ba. Rukunin mabiya Dalai Lama sun yi zagon-kasa ga "'yancin kai" da "dokokin shari'a" sosai, wato daga tushe ne suka lalata zaman jituwa a Tibet.

Rura wutar tashin-hankali ba sa taimaka wajen haifar da zaman jituwa, kuma ba zai samu goyon-baya daga wajen jama'a ba!(Murtala)