Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-08 09:56:16    
An cimma nasarar kai wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma

cri

Ran 8 ga wata, an cimma nasarar kai wutar gasar wasanin motsa jiki ta Olympic ta Beijing zuwa kololuwar Qomolangma, wannan shi ne karo na farko da aka kaiwa wutar wasannin Olympic zuwa Qomolangma watau babban dutse mafi tsayi a duniya, wanda tsawonsa ya kai mita 8844.43 a cikin tarihin gasar wasannin Olympic ta duniya.


A gun bikin "kaiwa wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma" da aka yi a wannan ranar, da sanyin safiya, mambobi 12 masu hawan dutse sun fara hawan kololuwar Qomolangma daga sansaninsu. Da misali karfe 9 da mintin 10 da safe agogon Beijing, masu dauke da wutar yola 4 sun cimma nasarar mika wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma. Tutar kwamitin wasannin Olympic na duniya da tutar kasar Sin da tutar gasar wasannin Olympic ta Beijing suna kadawa tare cikin iska a kololuwar Qomolangma.


Bayan da aka cimma nasarar kaiwa wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa kololuwar Qomolangma, za a mika wannan wutar zuwa birnin Lhasa a adana, kuma zuwan watan Yuni na shekarar da muke ciki, yayin da aka kaiwa wutar wasannin Olympic na Beijing zuwa Lhasa za a hada wadannan wuta biyu tare.(Bako)