Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 20:22:33    
Hu Jintao ya gana da shugabannin kasar Japan, kuma ya yi muhimmin jawabi kan dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin Sin da Japan

cri

Yau 7 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da sarkin kasar Japan Akihito a birnin Tokyo, kuma ya yi shawarwari tare da firayin ministan kasar Fukuda Yasuo. Daga baya kuma, Mr. Hu Jintao ya halarci liyafar cin abincin rana da muhimman kungiyoyin tattalin arziki na Japan suka yi don maraba da zuwansa, inda ya yi wani muhimmin jawabi.

A lokacin da yake ganawa da Sarki Akihito, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, tun fil azal, ya kasance da zumunci a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Japan. Kazalika kuma, Mr. Hu Jintao ya nuna yabo ga Sarki Akihito saboda yana mayar da hankali kan bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan.

A lokacin da yake yin shawarwari tare da Mr. Fukuda Yasuo, Mr. Hu Jintao ya jaddada cewa, yanzu dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan na kan sabon masomin tarihi, ya kamata bangarorin biyu su yi kokari tare, don kafa sabon hali na bunkasa dangantaka ta samun moriya ga juna a dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu.

Bayan shawarwarin kuma, bangarorin biyu sun cimma haddadiyar sanarwa game da ciyar da dangantaka ta samun moriya ga juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tskaanin Sin da Japan gaba. (Bilkisu)