Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 17:19:17    
Ana mika fitilar wasannin Olympic na Beijing a birnin Guangzhou na kasar Sin

cri
Da karfe 8 da minti 13 na safiyar ran 7 ga wata, an fara mika fitilar wasannin Olympic na Beijing a birnin Guangzhou da ke a kudancin kasar Sin. Ya zuwa yanzu, ana nan ana mika fitilar.

A birnin Guangzhou, an shirya bikin fara mika fitilar a cibiyar taron kasa da kasa mai suna Baiyun, an ratsa da fitilar a Dutsen Baiyun da Dakin Tunawa da Zhongshan, da kwatar Tianzi da babbar gadar Guangzhou da filin Zhuhai da sauran gine-ginen al'adu da shahararrun wurare masu ni'ima, za a isa dakin wasan motsa jiki na cibiyar wasanni mai suna Tianhe a karshe. Dukan tsawon hanyar da ake bi wajen mika fitilar ya kai kilomita 40.82.

An labarta cewa, masu mika fitilar wadanda yawansu ya kai 208 suna mika fitilar a birnin Guangzhou. Yang Jinghui, zakaran wasan yin tsalle cikin ruwa na wasannin Olympic ya zama na farko da ake mika fitilar, haka kuma Dong Zhaozhi wanda ya taba samun lambar azurfa ta wasan foil na kungiya-kungiya na wasannin Olympic ya zo na karshe ga mika fitilar. (Halilu)