Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:57:00    
Shugaba Hu Jintao ya yi tattaunawa da sarkin Japan Akihito da firaminista Yasuo Fukuda bi da bi

cri
A ran 7 ga wata da safe, sarkin kasar Japan Akihito ya shirya biki, don yin maraba da ziyarar shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ke yiwa kasar Japan. Daga baya kuma, shugaba Hu Jintao ya yi taron tattaunawa da firaministan kasar Japan Yasuo Fukuda.

Ran nan da karfe 9 na safe, agogon wurin, sarkin kasar Japan Akihito ya shirya bikin maraba da shugaba Hu Jintao a fadar sarki. Bayan bikin nan, sarkin Japan ya gana da shugaba Hu Jintao.

Daga baya kuma, shugaba Hu Jintao ya yi taron tattaunawa da firaminita Yasuo Fukuda. Domin kafa sabon hali da dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasar Sin da kasar Japan ke ciki, shugabanin kasashen biyu sun yin gwiwar tsara shirin nan gaba na raya dangantakar dake tsakaninsu cikin hangen nesa bisa manyan tsare-tsare, sun tabbatar manyan ka'idojin ba da jagorancin ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a sabon halin da ake ciki da kuma tabbatar da muhimman fannoni na hadin gwiwa da aka yi cikin matsakaicin lokaci da dogon lokaci a tsakanin kasashen biyu, kuma sun kafa tsarin raya huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Japan lami lafiya cikin dogon lokaci.

Shugaba Hu Jintao ya fara ziyarar aikinsa a kasar Japan a ran 6 ga wata, ziyarar sada zumunta a yanayin bazara za ta shafe kwanaki 5. Wannan kuma ya zama karo na farko ne da shugaba kasar Sin ke ziyara kasar Japan a cikin shekaru 10 da suka wuce. Ran nan kuma, shugaba Hu Jintao ya bayar da jawabi cewa, yana fatan za a iya yin amfani da ziyarar nan don kara zumunta da amincewar juna, da zurfafa hadin gwiwa, da tsara shirin makoma, da kuma kafa sabon hali da dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasar Sin da Japan ke ciki. Ran nan kuma, shugaba Hu Jintao ya gana da dangi da yayan abokanmu na kasar Japan da suka riga mu gidan gaskiya amma suka ba da babbar gudumowa ga aikin komar da huldar jakadanci tsakanin Sin da Japan kamar yadda ya kamata, kuma ya halarci liyafa da Yasuo Fukuda ya shirya masa. (Zubairu)