Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:41:46    
Ya kamata a rika yalwata da bunkasa al'adun gargajiya na Tibet, a cewar wani kwararren ilimin Tibet

cri
Kwanan baya, yayin da wani manazarcin sashen tarihi na cibiyar nazarin ilimin Tibet ta kasar Sin mai suna Zhang Yun ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewar, al'adun gargajiyar na Tibet wani bangare ne na nagartattun al'adun gargajiya na kasar Sin, wadanda ke kunshe da kyawawan fasahohi da ilimomi, kamata ya yi a rika yalwata da bunkasa su ba tare da tsayawa ba.

Zhang Yun ya ce, a cikin tarihin bunkasuwar al'adun gargajiya na Tibet, an samu kyawawan nasarori a fannoni da dama, ciki har da sanannun littattafai na gargajiya, da ilimin likitanci, da ilimin taurari da dai sauransu. Kazalika kuma, gidajen ibada da fadar sarakuna masu dadadden tarihi sun kasance muhimman abubuwa cikin kyawawan al'adun gargajiya na Tibet.

Zhang ya kara da cewar, rika bude kofa ga ketare, muhimmin dalili ne da ya sa aka samu bunkasuwar al'adun gargajiya na Tibet kwarai da gaske.

Yana ganin cewar, domin gadar nagartattun al'adun gargajiya na Tibet, kamata ya yi a rubanya kokari wajen koyonsu, da samu kyawawan abubuwa daga cikinsu, da rika bincikensu ba tare da kasala ba, da koyi fasahohi da hazikanci daga wajen kakan-kakaninmu, da wallafa kyawawan littattafan al'adu gargajiya, tare kuma da yada nagartattun al'adun gargajiya, ta yadda za su daukaka cigaban wayewar kai ta duk zamantakewar al'umma.(Murtala)