Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:17:18    
Mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
Ran 25 ga watan Afrilu bisa agogon wurin, wutar wasannin Olympic ta ci gaba da ziyararta a birnin Nagano na kasar Japan, an mika ta a ran 26 ga watan Afrilu.

A matsayinta na makwabciyar kasar Sin, Japan ita ma ta nuna matukar sha'awa kan wasannin Olympic. Game da wutar wasannin Olympic da kuma wasannin Olympic, dimbin masu rike wutar sun nuna ra'ayi kusan iri daya, wato suna sa ran sosai cewa, za a yi gasar wasannin Olympic a kasar Sin da ke makwabtaka da kasarsu. Madam Mizuki Noguchi, shahararriyar 'yar wasan gudun Marathon ta Japan, wadda kuma ta zama zakara a cikin shirin gudun Marathons na gasar wasannin Olympic ta Athens ta yi zumudi sosai ta ce,'A matsayina na mai rike da wutar ta karshe, hankalina bai iya kwanta ba. Amma na ji farin ciki saboda na iya kunna wutar da aka mika mini. Ina fatan za a sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic a Beijing cikin zaman lafiya. Wasannin Olympic ita ce alamar zaman lafiya. A gun gasar wasannin Olympic, kowa da kowa na da burin shimfida zaman lafiya. Ina fatan za a sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic. Ni ma zan shiga gasar gudun Marathons a Beijing. Zan yi kokari. Wannan shi ne kasaitacciyar gasa da a kan yi sau daya a ko wadanne shekaru 4, haka kuma, shi ne babban dandamali ga dukkan 'yan wasa. Ina fatan 'yan wasa za su mai da hankulansu domin samun maki mai kyau.'

Shiuzo Matsuoka, shahararren dan wasan kwallon tennis na Japan, shi ma ya zama mai rike da wutar a wannan karo. Bisa abubuwan da ya fada, an iya gano kaunar da yake nunawa kan wasannin motsa jiki da kuma kan zaman lafiya. Ya ce,'An mayar da shimfida zaman lafiya tamkar babban taken aikin mika wutar a wannan karo. Ni ma ina fatan za a wanzar da ainihin jituwa a duk duniya. A lokacin da nake gudu tare da wutar, ina fatan za a sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic a Beijing cikin zaman lafiya, ina yin addu'a kan wannan.'

Bayan Nagano na Japan da kuma birnin Seoul na kasar Korea ta Kudu da birnin Pyongyang na kasar Korea ta Arewa da kuma birnin Ho Chi Minh na kasar Vietnam, wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami nasarar dawowa kasar Sin. Yanzu ana mika wa juna wutar a duk fadin kasar Sin. Dukkan Sinawa da wadanda ke kaunar zaman lafiya a duk duniya suna fatan wutar za ta dawo Beijing yadda ya kamata, kuma za a shirya gasar wasannin Olympic cikin cikakkiyar nasara.(Tasallah)