Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:15:24    
An mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a dukkan nahiyoyi 5 na duniya

cri
Tun daga ran 21 zuwa ran 27 ga watan Afrilu, an ci gaba da mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a nahiyoyin Asiya da Oceania. Musamman ma, bayan da aka samu nasarar mika wutar a birnin Canberra, hedkwatar kasar Australia a ran 24 ga watan Afrilu, an tabbatar da mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a dukkan nahiyoyi 5 na duniya.

Bayan da aka kammala mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a biranen Muscat da Islamabad da New Delhi da kuma Bangkok lami lafiya, wutar ta yi ban kwana da Bangkok mai kyan gani, ta sauka birnin Kuala Lumpur, hedkwatar kasar Malaysia a ran 20 ga watan jiya bisa agogon wurin.

Jama'ar Malaysia sun nuna sha'awa sosai kan shiga aikin mika wutar wasannin Olympic. A ranar kafin a mika wutar a hukunce, an yi gasar gudu game da mika wutar a Kuala Lumpur. Sheikh Mustafa Shukor, dan sama-jannati na farko na Malaysia ya zama daya daga cikin masu rike da wutar. A ran 21 ga watan Afrilu bisa agogon wurin, an sami nasarar mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Kuala Lumpur.

Tare da zumunci mai karko da jama'ar Malaysia ke nunawa, an kai wa wutar a birnin Jakarta, hedkwatar kasar Indonesia. An fara mika wa juna wutar a ran 22 ga watan Afrilu da yamma bisa agogon wurin.

Jakarta, birni ne da ya sada zumunci a tsakaninta da birnin Beijing. Dukkan biranen 2 sun dora muhimmanci kan raya wasannin motsa jiki, sun kuma yi mu'amala sosai a fannonin al'adu da harkokin birni. A matsayinsa na mai rike da wutar ta farko a Jakarta, Fauzi Bowo, shugaban Jakarta ya ji alfahari sosai ya ce,'Na ji farin ciki da alfahari saboda na zama mai rike da wutar na farko. Zan yi iyakacin kokarina domin samun nasarar kammala aikina.'

A kan hanyar mikawa wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, an yi ta jin ihu cikin murna daga ko wane 'yan kallo. A cikin wadannan mutanen da suka yi ihu domin karfafa gwiwar Beijing, akwai wani muhimmin rukuni, wato wakilan masana'antu masu jarin kasar Sin. Yawancinsu suna aiki a Indonesia a wani tsawon lokaci, sun kara fahimtarsu kan wannan kasa kadan. Zong Qingsheng da ke aiki a kamfanin aikin sadarwa na Zhongxing ya ce,'A ganina, Sinawa mazaunan wurin suna mara wa gasar wasannin Olympic ta Beijing baya kwarai. Mun ji alhafari sosai kan wannan. Ina jin dadin zamana a Jakarta, ana nuna mana Sinawa zumunci.'

Kamar yadda Mr. Rita Subowo, shugaban kwamitin wasannin Olympic na Indonesia ya fada cikin Sinanci a gun bikin samun nasarar mikawa wutar, wato ran abokantakar da ke tsakanin Sin da Indonesia ya dade! Bayan Jakarta, an kai wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Canberra, hedkwatar kasar Australia ran 22 ga watan Afrilu da dare bisa agogon wurin cikin jirgin sama na musamman, an ci gaba da aikin wanzar da jituwa a duk duniya. Wutar ta bai wa jama'ar Indonesia ruhun wasannin Olympic, wato zaman lafiya da abokantaka.

Canberra na cikin kudu maso gabashin Australia, ma'anarta a ita ce wurin da aka taru a bakin 'yan kabilar Aborigines. Canberra, wani kyakkyawan birni ne inda akwai wuraren yawon shakatawa da lambunan furanni a ko ina. An tsara shi yadda ya kamata, ya nuna abu mafi nagarta da Australia ke da shi.

A matsayin birni daya tak a nahiyar Oceania da aka mika wa wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, mazaunan Canberra da Sinawa 'yan kaka gida a wurin da kuma daliban kasar Sin da ke karatu a Australia sun nuna matukar sha'awa kan karfafa gwiwar mika wa juna wutar. Sa'an nan kuma, 'yan kabilar Aborigines sun yi bikin gargajiya domin maraba da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing.

'Wannan shi ne biki da muka shirya domin tunawa da kasar da muke tsayawa a kai. Muna muku maraba da zuwa kasar da kakan kakaninmu suka taba zama.'

John Coates, shugaban kwamitin wasannin Olympic na Australia ya bayyana cewa,'Wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta tuna mana da gasar wasannin motsa jiki ta sada zumunci da aka yi a birnin Melbourne a shekarar 1956 da kuma gasar wasannin Olympic ta Sydney a shekarar 2000. Sa'an nan kuma, na tuna muku da cewa, Australia na daya daga cikin kasashe 2 kawai da suka halarci dukkan gasannin wasannin Olympic na zamani. Bayan kwanaki 100 ko fiye, 'yan wasa 414 za su sake shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing a madadin dukkan jama'ar Australia.

Ran 24 ga watan Afrilu bisa agogon wurin, an sami nasarar mika wa wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Canberra, wutar gasar wasannin Olympic ta kone a nahiyar Oceania, ta haka, an tabbatar da mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a dukkan nahiyoyi 5 na duniya.(Tasallah)