Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:11:28    
Mai fassara kuma mai tsara rubutattun wakoki na kasar Sin mai suna Cai Shu

cri

Ba da dadewa ba wani mai tsara rubutattun wakoki kuma mai rubuta bayanai na kasar Faransa Mr Yves Bonnefoy wanda ke da shekaru 84 da haihuwa yanzu ya sami lambar yabo mai muhimmanci ta Turai da aka kira "The Franz Kafka Prize" dangane da dabi'a a shekarar 2007. Da mai tsara wakoki na kasar Sin Mr Shu Cai da ke da shekaru 42 da haihuwa ya ji labarin nan, sai ya yi farin ciki sosai , duk saboda a cikin shekaru da yawa da suka wuce, ya taba gabatar da Mr Yves Bonnefoy ga masu karantawa na kasar Sin, a wannan karon da Mr Yves Bonnefoy ya sami lambar yabon, an bayyana cewa, Mr Shu Cai na da basira irin ta mai fasarrawa kuma mai tsara wakoki.

Shu Cai shi ne wani mai bincike na hukumar yin bincike kan dabi'ar kasashen waje ta kasar Sin, amma kafin wannan, ya taba zama wani dan diplomasiya na kasar Sin da ke wakilci a kasashen Afrika, kuma ya taba zama babban shugaba na wani kamfanin kasuwanci. Ya bayyana cewa, tun da nake shiga makarantar sakandare, sai na soma kaunar rubutattun wakoki na zamanin yau. Kuma na taba rubuta wasu rubutattun wakoki bisa salon rubutattun wakoki na zamani aru aru. Amma bayan da na shiga cikin wata jami'a a birnin Beijing, sai na canja halin da nake ciki, tare da abokaina na jami'ar ne muka shirya wata kungiyar dabi'a wadda take bayar da mujalla, sunanta shi ne "Test" , daga nan sai na soma rubuta rubutattun wakoki cikin tsanaki.

Abin bakin ciki sosai gare shi shi ne rasuwar mahaifiyarsa a lokacin da yake karami, sa'anan kuma kakarsa ita ma ta rasu, wannan ya yi masa tasiri sosai a lokacin da ya ke girma. A shekarar 1983, ya shiga jami'ar koyon ilmin harsunan waje ta birnin Beijing daga lardin Fujian, a daidai wannan lokaci, kasar Sin ta soma yin kwaskwarima a fannoni da yawa, kuma an sami kwararrun dabi'ar kasar Sin da masu tsara rubutattun wakoki da yawa, daga nan Shu Cai ya soma bayar da rubutattun wakokinsa. Ya bayyana cewa, a shekarar 1986, na bayar da rubutattun wakoki ba da yawa ba, , amma wata rubutaciyyar wakar da na bayar a shekarar 1987 ta zama muhimmiyyar wakar da na tsara , wadda take da lakabi haka: tsuntsaye biyu, an tattara wakar cikin wani littafi.

Bayan da ya gama karatu a jami'ar, sai ya shiga aikin yin cinikayya da kasashen waje. Dayake ya taba koyon harshen Faransanci, shi ya sa an taba tura shi zuwa kasar Senegal don ya zama wani dan Diplomasiya na kasar Sin, zaman rayuwarsa a Afrika ya ba da tasiri sosai gare shi wajen rubuce-rubuce.Ya ce, In ba ka taba tafiya zuwa kasashen Afrika ba, to mai yiyuwa ne za ka iya ganin cewa, kasashen Afrika suna baya baya a duniya, amma bayan da na yi zama a Afrika, sai ra'ayina ya canja. Kai, babbar nahiyar Afrika tana da halittun da ba a taba dakushe su ba, kuma ana shimfida su yadda ya kamata sosai da sosai ba tare da karfin 'yan adam ba. Na taba sauka a kasashen yammacin Afrika, al'adunsu sun kawo wa mutane faranta rai sosai, sa'anan kuma na ji cewa, kamar yadda irin wannan abu ya riga ya shiga cikin jinina, ya kuma zama wani abu mai yakini gare ni, Halin da mutanen Afrika suke ciki na faranta rai ya burge ni sosai da sosai.

Bayan shekaru hudu da ya yi aiki a Afrika, sai ya koma gida a shekarar 1994, sa'anan kuma ya bayar da wani kundin rubutattun wakoki wanda a ciki da akwai wakokin da ya rubuta yawansu ya kai 150, Mr Shu Cai ya rubuta wadannan wakoki ne cikin shekaru kusan goma.

Don ci gaba da yin nazari a kan rubutattun wakoki, Mr Shu Cai ya bar aikinsa a wani kamfani, sa'anan kuma ya kama aikin bincike a hukumar yin nazari kan dabi'ar kasashen waje , a wani fanni, yana rubuta wasu wakoki, a wani fanni daban kuma yana fassara wasu wakokin kasashen waje, ba sau daya ba, ba sau biyu ba ya tafi kasashen waje don yin ma'amala da masu tsara rubutattun wakoki na kasashen waje, ya ce, abokansa wajen rubutattun wakoki na da yawan gaske a duk duniya a ko'ina.(Halima)