Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 13:48:53    
Kafofin watsa labaru na kasar Koriya ta kudu da na kasar India sun yabawa ziyarar sada zumunta da shugaba Hu Jintao ya yi

cri

A ran 6 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya fara ziyarar aikinsa a kasar Japan, watau ya fara ziyarar sada zumunta ta kwanakin 5. A kwanakin nan, kanfanonin yada labaru na kasar Koriya ta kudu da na kasar India sun bayar da labaru bi da bi, inda suka yabawa ziyarar sada zumuntar nan.

A ran 6 ga wata, jaridar "Joongang Daily News" ta kasar Koriya ta kudu ta bayar da labari cewa, ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi za ta zama kyakkyawar dama ta kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Japan. Ziyarar sada zumuntar nan za ta sa kaimi ga dangantakar bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasar Sin da Japan a dukkan fannoni kamarsu fannin siyasa, da fannin tattalin arziki, da dai sauransu, kuma za ta canja halin da harkokin waje na kasashen biyu, har ma na yankin arewa maso gabashin Asiya ke ciki.

Ran nan kuma, jaridar "Chosun Ilbo" ta kasar Koriya ta kudu ta bayar da labari cewa, shugaba Hu Jintao ya yi ziyararsa lokacin da ake cika shekaru 30 da kasashen Sin da Japan suka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da zumunta, wannan zai ba da taimako ga kyautata dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Japan, da kuma ciyar da dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasar Japan gaba.

Ban da wannan kuma, kamfanin watsa labaru mai suna "Asia News Agency" na kasar India ya bayar da labari a kwanakin nan cewa, ziyarar nan da shugaba Hu Jintao ya yi ta zama ziyara a karo na farko ne da shugaban kasar Sin ke yiwa kasar Japan a cikin shekaru 10 da suka wuce.

Jaridar "Daily Statesman" ta kasar India da aka buga a ran 4 ga wata kuma ta bayar da labari, inda ta ce, ko shakka babu, ziyarar shugaba Hu Jintao ta kwanaki 5 a kasar Japan za ta zama muhimmin mataki da bangarorin Sin da Japan suka dauka don ci gaba da kyautata kuma raya dangantaka dake tsakaninsu biyu. (Zubairu)