Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 12:44:07    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da abokai na Japan

cri
A ran 6 ga watan Mayu, da isowarsa a birnin Tokyo na kasar Japan domin soma yin ziyararsa ta aiki a kasar Japan, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da yara da dangi na nagartattun 'yan siyasa wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen raya huldar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Japan. A gun ganawar, Mr. Hu ya ce, gwamnati da jama'ar kasar Sin ba za su manta da wadannan abokai na kasar Japan ba har abada. "Ana iya shiga kyakkyawan halin da ake ciki kan huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan, ba za a iya mantawa da kokarin da kakanin-kakaninku suka yi ba. Mu Sinawa muna da wata karin magana da cewa, 'lokacin da kake shan ruwan rijiya, kada ka manta da mutane wadanda suka hako wannan rijiya'. Kakanin-kakaninku sun bayar da gudummowa sosai wajen raya huldar sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Japan, mu Sinawa za mu tuna da su har abada."

Wadannan nagartattun 'yan siyasa na kasar Japan da suka bayar da gudummowa sosai wajen raya huldar sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Japan suna kunshe da marigayi Tanaka Kakuei, tsohon firayin ministan kasar Japan wanda ya tsai da kudurin komar da huldar da ke tsakanin Sin da Japan kamar yadda ya kamata da marigayi Ohira Masayoshi, tsohon firayin ministan kasar Japan wanda ya tsai da kudurin samar wa kasar Sin rancen kudi domin neman cigaban kasar Sin tare da marigayi Sonoda Hiroyuki, tsohon ministan harkokin waje na kasar Japan wanda ya wakilci gwamnatin kasar Japan ya sa hannu a kan yarjejeniyar sada zumunta irin ta zaman lafiya a tsakanin Japan da Sin yau da shekaru 30 da suka gabata.

Madam Tanaka Makiko, 'yar marigayi firayin minista Tanaka Kakuei na kasar Japan tana tafiyar da harkokin siyasa a kasar Japan har yanzu. Ta ce, "Sabo da muna zama a wani gidan 'yan siyasa, dukkan iyalanmu muna mai da hankula sosai kan harkokin kasar Sin. A cikin wadannan shekaru da yawa da suka gabata, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta sha wahala sosai. Amma a nan gaba, ni ko 'yan siyasa na iyalanmu za mu ci gaba da yin kokarinmu domin kara raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu a ko da yaushe. Idan ubana ya yi zama a duniya yanzu, tabbas ne zai yi fata za a samu nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing. Gasar wasannin Olympic ta Beijing wata kasaitaciyyar gasa ce ta duk duniya. Ina fatan za ta samu nasara." 

Lokacin da yake ganawa da wadannan yaran tsoffin abokai na Japan, Hu Jintao ya yaba su kwarai domin har yanzu suna kokarin sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Japan. Mr Hu ya ce, "Na gode muku kwarai da gaske sabo da kuna bayar da gudummoawarsu sosai wajen sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Japan a cikin dogon lokacin da ya gabata."

A shekarar 1984, gwamnatin kasar Sin ta taba gayyatar matasa dubu 3 na kasar Japan da su kawo wa kasar Sin ziyara. A wancan shekara, madam Seri Yoko, wata mawakiyar kasar Japan ta halarci wannan biki tare da diyyarta wadda ta kai shekaru 2 da haihuwa kawai. Lokacin da take tunawa da wannan biki, madam Seri Yoko ta ce, "A lokacin da na kai ziyara a kasar Sin a shekarar 1984, diyyata ta kai shekaru 2 da haihuwa kawai. Amma yanzu tana kuma yin aikin kide-kide kamar ni. Tana kuma kokarin yin amfani da kide-kide da wakoki domin sada zumunta a tsakanin kasashen Japan da Sin. Mu kan fadi cewa, kide-kide suna karbuwa a duk fadin duniya. Ina fatan yaranmu za su ci gaba da yin musaye-musaye kan al'adu da kide-kide a tsakanin kasashen biyu."

Game da makomar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan, Mr. Hu ya ce, "Yanzu huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan tana kan sabon matsayi, kuma tana fuskantar sabuwar damar neman cigaba. Makasudin yin ziyarata a kasar Japan shi ne ina son hada kan bangaren Japan domin bayar da kokarinmu tare wajen raya wata sabuwar huldar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen Japan da Sin daga dukkan fannoni."   (Sanusi Chen)