Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 21:34:55    
Mr Hu Jintao ya sauka birnin Tokyo don fara yin ziyara a yanayin bazara

cri
Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Japan ta yi masa ne, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya sauka birnin Tokyo a yau Talata don fara yin ziyarar aiki a kasar Japan, wato ziyarar kwanaki biyar a yanayin bazara.

Wannan ziyarar da wani shugaban kasar Sin ya sake yi wa kasar Japan bayan shekaru 10 da suka wuce.

Bayan da ya sauka a filin jirgin sama mai suna Haneda na kasar Japan, Mr Hu Hintao ya bayar da jawabi a rubuce cewa, shekarar nan shekara ta 30 ce da aka daddale yarjejeniyar zaman lafiya da aminci a tsakanin Sin da Japan. Ya kasance da sabuwar dama wajen kara yalwata hulda a tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, yana fatan za a kara amincewa da juna, da kara dankon aminci, da inganta hadin gwiwa, da tsara makoma ta hanyar wannan ziyara, ta yadda za a bude wani sabon shafi ga yalwata dangantakar moriyar juna a tsakanin Sin da Japan daga manyan tsare-tsare. Ya yi imani cewa, bisa kokarin da kasashen biyu ke yi tare, tabbas ne, ziyarar za ta cim ma manufar da aka tsara.

A ranar da ya sauka a birnin Tokyo, Mr Hu Jintao ya gana da dangi da zuriyar baya na aminanmu da dama na kasar Japan wadanda suka taba ba da babban taimako wajen kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da Japan. (Halilu)