Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 20:48:37    
Manyan gidajen Ibada na jihar Tibet sun shirya gaggarumin biki don yin fatan alheri ga wasannin Olympic na Beijing

cri
A kwanakin nan, manyan gidajen Ibada na jihar Tibet ta kasar Sin sun shirya gagaruman biki don yin addu'a ga tabbatar da zaman lafiya a duniya da fatan wasannin Olympic na Beijing zai sami cikakkiyar nasara.

A ran 5 ga wata, gidan Ibada mai suna Drepung Monastery a Turanci da ke a karkarar yammacin birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet ya shirya gagaruman biki bisa al'adar gargajiya. Sufayen addinin Buddha sama da 400 sun karanta nassin littattafan addinin Buddha tare.

Dampa Lungdo, malami mai koyar da littattafan addinin Buddah wanda shekaraunsa suka kai 80 da haihuwa ya bayyana cewa, yana jin matukar farin ciki da iya shirya gagaruman biki cikin zaman jituwa da kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ya kara da cewa, mu tarin sufaye suna addu'a don yin fatan zaman lafiya a duniya, da yin fatan jama'a suna jin dadin zamansu cikin kwanciyar hankali, da yin fatan kasarmu za ta kara kasaita, da kuma yin fatan wasannin Olympic na Beijing zai sami cikakkiyar nasara.

A ran 30 ga watan jiya wato sauran kwanaki 100 da za a shirya wasannin Olympic na Beijing, sufayen addinin Buddha sama da 350 na gidan Ibada mai suna Sera wanda ke tazarar kilomita 3 daga arewacin fadar Potala a birnin Lhasa su ma sun taba shirya irin wannan gagarumar salla. (Halilu)