Bisa gayyatar da aka yi musu, zakarun wasannin Olympic na kasar Sin sama da 10 sun sauka wuri mai suna Jiuzhaigou na lardin Sichuan a ran 5 ga wata, inda suka bakunci 'yan kabilar Tibet, sun shiga cikin gidajen Ibada na kabilar, sun yi addu'a tare da sufaye don yin fatan alheri ga wasannin Olympic na Beijing.
A cikin gidan Ibada mai suna Daji na 'yan kabilar Tibet da ke a wurin, da babbar murya, zakarun wasannin Olympic da sufayen kabilar Tibet suka yi kirari cewa, "nasara za ta tabbata ga wasannin Olympic na Beijing. Malam Gao Min, sarauniyar wasan yin dake cikin ruwa, kuma zakarar wasannin Olympic wadda ta hallarci sallar, ta ce, ta yi matukar farin ciki da ganin 'yan'uwanmu na kabilar Tibet da yawa kamar haka suke addu'a tare da ita don kawo alheri ga wasannin Olymic na Beijing.
Wani sufin gidan Ibada na Daji ya bayyana cewa, bisa matsayinsa na sufi mai kishin kasa da addini, da zuciya daya ce, shi da sauran sufaye na gidan Ibadan suke fatan wasannin Olympic na Beijing zai sami nasara, wannan wata alama ce mai muhimmanci ga zaman jituwar al'ummar kasar Sin. (Halilu)
|