|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-05-06 17:12:38
|
An yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a lardin Hainan
cri
Tun daga ranar 4 zuwa ranar 6 ga wata ne aka kawo fitilar wasannin Olympics na Beijing a babban yankin kasar Sin, kuma an soma yawo da fitilar a birane da dama na lardin Hainan da ke kudancin kasar.
A ranar 4 ga wata da safe, an kunna fitilar wasannin Olympics a birnin Sanya, wani shahararren birnin yawon shakatawa na lardin Hainan, wannan ya nuna cewa, an soma bikin yawo da fitilar wasannin Olympics a babban yankin kasar Sin a hukunce.
A ranar 5 ga wata, an kawo karshen yawo da fitilar a zanguna guda biyar da ke wurare uku na lardin Hainan, wato Wu Zhishan, da Wanning, da kuma Qionghai.
A yau ranar 6 ga wata da safe da karfe 8 da minti goma kuma, an soma yawo da fitilar a birnin Haikou, hedkwatar lardin Hainan, birnin Haikou shi kuma zango ne na karshe da aka yi yawo da fitilar a lardin Hainan. (Bilkisu)
|
|
|