Ya zuwa karshen shekarar da ta wuce, manoma da makiyaya wadanda yawansu ya kai dubu 112 na jihar Tibet sun samu gidaje masu inganci sakamakon ayyukan samar da gidajen kwana da gwamnatin Sin ke yi a kauyukan jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar.
Wakilinmu ya samu wannan labari ne a ran 6 ga wata daga cibiyar binciken ilmin Tibet.
An ce, jihar Tibet ta fara gudanar da aikin samar da gidajen kwana ga manoma da makiyaya daga shekarar 2006, bisa shirin da aka tsayar an ce daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, za a kyautata gidajen kwana domin iyalan manoma da makiyaya da yawansu ya kai dubu 220, ta yadda manoma da makiyaya da yawansu ya kai kashi 80 bisa 100 za su iya samun gidaje masu inganci.
An ce, aikin da ake yi ba ma kawai domin samar da gidajen kwana ga manoma da makiyayya na jihar Tibet ba, har ma za a kyautata sharudan zaman yau da kullam daga dukkan fannoni, ciki har samar da ruwan sha da wutar lantarki da kuma saurarar labaru ta rediyo. Kuma ta hanyar yin wannan aiki za a ba manoma da makiyaya damar samun kudin shiga da yawa. (Umaru)
|