Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:30:49    
Gidan marayu musulmai na farko na jihar Ningxia

cri

An kafa gidan marayu musulmai na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin a ran 20 ga watan Yuni na shekarar nan da muke ciki, wanda yake gundumar Xingjing da ke karkashin jagorancin birnin Yinchuan, hedkwatar jihar, wannan shi ne gidan marayu musulmai na farko na jihar, kuma fadinsa ya kai murabba'in mita 2100, inda ake cikin shirin karbar marayu 300.

Abdu Al Halik, shugaban kungiyar jin kai ta musulunci ta jihar Ningxia ya bayyana cewa, kwamitin kula da musulmai na kasashen Asiya na kungiyar jin kai ta musulunci ta kasa da kasa ta kasar Kuwait shi ne ya samar da kudin Sin wato Yuan miliyan 1.8 don hadin gwiwa tare da kungiyar jin kai ta musulunci ta Ningxia wajen kafa wannan gidan marayu. Kuma ya gaya mini cewa, dalilin da ya sa ya kafa gidan marayu shi ne sabo da shi wani maraya ne, a lokacin yarantakarsa ya sha wahala sosai, shi ya sa bayan da ya girma, yana da aniyar kafa wani gidan marayu domin su iya samun kyakkyawar kulawa da kuma damar samun ilmi. Ban da wannan kuma ya kara da cewa,

"bayan da na samu aikin yi, har kullum na kan gudanar da ayyukan jin kai ga musulmai. Mun kan tattara kudade daga kasashen da ke shiyyar gabas ta tsakiya don shimfida hanya da haka rijiyoyi da samar da kudin taimko ga 'yan makaranta na jihar Ningxia. A waje daya kuma mun kan samar da kudi ga marayu, amma lokacin da muke yin bincike, mu gano cewa, a hakika dai wasu marayu ba su iya samun wadannan kudade ba. Ganin haka, mun yi zaton cewa, ya fi kyau mu kafa wani gidan marayu da kanmu, ta yadda za a iya yin amfani da kudaden da muka tattara wajen kula da marayu. Bugu da kari kuma, muddin kowa ya mai da hankali kan mutane marasa galihu domin su iya samun damar samun ilmi da jin dadin zama, al'ummarmu za ta iya samun jituwa."

Duan Juan wata malama ce ta gidan marayu musulmai na jihar Ningxia, lokacin da na gan ta, na ji mamaki sosai, ita wata budurwa ce wadda shekarunta ya kai 22 da haihuwa kawai. A shekarar da ta gabata, ta gama karatunta daga sashen harshen Sinanci na jami'ar Ningxia, kuma ta gaya mini cewa, dalilin da ya sa ta zo gidan marayu shi ne sabo da ta nuna tausayi sosai ga wadannan yara, kuma kamar yadda waliyai su kan ce, idan an kula da marayu, to zai iya yin zama tare da Allah har abada. Ban da wannan kuma Duan Juan ta bayyana cewa,

"lokacin da wadannan yara suke gidajensu, kakaninsu suna iya samar da isasshen abinci gare su, amma ba su iya ba da tabbaci gare su wajen samun ilmi. Bayan da suka shiga gidan marayu, mun fi dora muhimmanci kan ba da ilmi domin su iya zama kwararru a nan gaba."

Domin cimma wannan buri, gidan marayu musulmai na jihar Ningxia ya mai da hankali sosai kan kwarewar malamai wajen aiki, dukkan malamai da aka dauka sun gama karatu daga jami'o'i, ban da wannan kuma shugaba Abdu ya tuntubi hukumar kula da ilmi ta wurin domin marayun su iya shiga makarantu. Kuma ya gaya mini cewa,

"shekarun marayun da muka dauka ya kai 3 zuwa 10 da haihuwa. Idan shekarunsu bai kai 6 da haihuwa ba, to malamai na gidan marayu za su ba da ilmi, idan shekarunsu ya dace da shiga makarantun firamare, za mu kai su zuwa makarantu domin samun ilmi. Haka kuma idan sun gama karantu daga makarantar sakandare, kuma suka ci jarrabawar shiga jami'a, to za mu ci gaba da samar da kudin karatu gare su domin su iya kara ilminsu, in ba su ci jarrabawar ba, sai su shiga makarantar koyar da ilmin sana'o'i da kungiyar jin dadin zaman musulmai ta Ningxia ta kafa, daga baya kuma za mu tallafa musu wajen samun guraban aikin yi."(Kande Gao)