Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 08:40:50    
Shugaban kasar Sin ya gaishe da 'yan Japan masu karanta mujella ta "Kasar Sin ta Jama'a"

cri
A jajibirin yin ziyararsa a kasar Japan, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gaishe da 'yan Japan wadanda suke karanta mujella "Kasar Sin ta Jama'a". A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya wakilci jama'ar kasar Sin ya nuna wa jama'ar Japan dimbin gaisuwa da fatan alheri.

Mr. Hu ya ce, bayan da aka kulla yarjejeniyar sada zumunta da shimfida zaman lafiya a tsakanin kasashen Sin da Japan yau da shekaru 30 da suka gabata, kasashen biyu sun samu babban sakamako kan yadda suka yi musanye-musanye na sada zumunta da hadin guiwa irin ta moriyar juna a tsakaninsu a fannoni daban daban. An kuma kawo wa jama'ar kasashen biyu moriya irin ta a-zo-a-gani. Wannan yarjejeniya ta kuma taka rawa sosai wajen raya wadannan kasashen biyu. Ya kamata jama'ar kasashen Sin da Japan su yabawa wadannan sakamako tare.

Mr. Hu ya kara da cewa, bayan shekaru 20 da suka gabata, za a sake yin gasar wannin motsa jiki ta Olympics a Asiya. Sabo da haka, wannan gasar wasannin Olympics ce ta Asiya kuma da ta duk kasashen duniya. Bugu da kari kuma, a zahiri ne Mr. Hu yana fatan jama'ar kasashen Sin da Japan za su kara sada zumunta a tsakaninsu har abada. (Sanusi Chen)