Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 14:30:08    
Shugaba Hu Jintao zai kai ziyara kasar Japan

cri
Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Japan ta yi masa ne, daga ran 6 zuwa ran 10 ga wannan wata, shugaba Hu jintao na kasar Sin zai zai ziyarar aiki a kasar Japan. Wannan ya zama karo na 2 ke nan da shugabannin kasar Sin suka kai ziyara Japan bayan shekaru 10 da suka wuce. A gabannin ziyararsa, a nan birnin Beijing Mr. Hu ya yarje tambayoyin da wakilan kafofin yada labaru 16 da ke nan birnin Beijing suka yi masa tare, inda ya bayyana cewa, ziyarar da zai kai Japan wata ziyara ce ta yanayin bazara mai kyau, yana fatan ta hanyar yin wannan ziyara za a ciyar da dangantakar samun moriyar juna bisa muhimman tsare-tsare kuma daga duk fannoni tsakanin Sin da Japan gaba. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta cikakken bayani game da wannan labari. "Ziyarar da zan yi a wannan gami a daidai lokacin furanni ke toho, wato a yanayin bazara mai kyau, ina fatan da zuciya daya cewa zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen 2 wato Sin da Japan zai dade har abada."

A farkon lokacin zantawa da manema labaru da aka yi a ran 4 ga wata, shugaba Hu Jintao ya yi murmushi ya roki dukkan maneman labaru da ke wurin da su isar da sahihiyar gaisuwarta da kyakkyawan fatan alheri da yake nuna wa jama'ar Japan.

Shekarar nan shekara ce ta cikon shekaru 30 da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aminci tsakanin Sin da Japan. A gun taron taron manema labaru, Mr. Hu Jintao ya yi jinjina sosai ga ci gaban da aka samu cikin shekaru 30 da suka wuce wajen dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan, kuma ya bayyana cewa, ci gaban da aka samu wajen dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 ba ma kawai ya kawo hakikaniyar moriya ga jama'ar kasashen 2 ba, kuma ya ba da muhimmin taimako ga zaman lafiya da dorewa da wadata na Asiya da duk duniya baki daya. Ya ce, "Hakikanan abubuwa su tabbatar da cewa, bunkasa dangantakar aminci ta makwabtaka cikin dogon lokaci tsakanin Sin da Japan yana dacewa da babbar moriya ta kasashen 2 da jama'arsu. Makasudin ziyarar da zan yi a kasar Japan shi ne kara amincewa juna da dankon zumunci da hadin gwiwa da hangen gaba, da sa kaimi ga dangantakar samun moriyar juna bisa muhimman tsare-tsare kuma daga duk fannoni tsakanin Sin da Japan.

Da wuyara kauce wa wasu matsalolin da suka bullo cikin yunkurin bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa, haka ma ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan. A kan wannan magana, Mr. Hu Jintao ya nanata cewa, ya kasance da wasu bambancin ra'ayoyi tsakanin kasa da kasa ba abu mamaki ba ne, amma muhimmin abu shi ne ya kamata a nemi bakin zare domin daidaita sabani da matsalolin da ke tsakaninsu. Ya ce, "Abu mai muhimmanci shi ne, ya kamata bangarorin 2 su yi shawarwari cikin sahihanci, da yin musayar ra'ayoyinsu cikin aminci, kuma su sami ra'ayi daya idan suna iyawa, im ba haka ba ya fi kyau su girmama juna, kuma su yi kokari tare domin kara dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen 2, da kiyaye babban batun bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 tare."

Mr. Hu Jintao yana cike da imani ga nasarar da zai samu a gun wannan ziyarar da zai kai Japan. Ya bayyana cewa, yana fatan yin saduwa a tsakaninsa da sarkin kasar Japan, da yin musayar ra'ayoyi sosai a tsakaninsa da firaminista Yasuo Fukuda na kasar kan dangantakar da ke tsakanin bangarorin 2 da sauran matsalolin da ke jawo hankulansu duka, ya hakakke cewa, bisa kokarin da bangarorin 2 ke yi tare, ba shakka ziyararsa za ta iya samun nasarar da aka tsammata. (Umaru)