Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-04 17:35:02    
Ziyarar aiki da zai yi a Japan, za ta zama ziyarar karfafa dangantaka a tsakanin Sin da Japan, in ji shugaba Hu Jintao na kasar Sin

cri

Yau 4 ga wata, a lokacin da manema labaru daga kafofin watsa labaru guda 16 na kasar Japan da ke nan birnin Beijing suka kai masa ziyara tare, don jin ta bakinsa, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ce, ziyarar aiki da zai kai a kasar Japan, za ta zama wata ziyarar karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Mr. Hu Jintao ya ce, makasudin ziyarar shi ne, domin kara nuna amincewa ga juna, da karfafa sada zumunci, da zurfafa hadin gwiwa, da shirya makoma, da kuma sa kaimi ga dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan da ta samu moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Ya yi imani cewa, a karkashin kokarin da bangarorin biyu suka yi tare, ko shakka babu ziyarar za ta samu sakamakon da aka yi hasashe.

Kazalika kuma, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, a yunkurin bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa, abin da ya fi muhimmanci shi ne, bangarorin biyu su nuna gaskiya ga juna, da yin mu'ammala ta sada zumunta, da kasance da ra'ayi daya da na bambanci tare, da kuma sa kaimi ga sada zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kiyaye halin bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Har wa yau kuma, a jaridar People's Daily da aka buga a yau 4 ga wata, Mr. Cui Tiankai, jakadan kasar Sin da ke Japan ya yi bayani cewa, ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi, tana da muhimmanci sosai, ta nuna cewa, gwamnati da shugabannin kasar Sin suna mai da hankali sosai kan kasar Japan, kuma suna son kara bunkasa kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Japan. (Bilkisu)