Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-02 20:04:10    
An yi amfani da kimiyya da fasaha na zamani don tabbatar da kunna wutar gasar wasannin Olympics a kolin dutsen Qomolangma

cri

Aikin mika wutar gasar wasannin Olympics a dutsen Qomolangma yana daya daga cikin muhimman ayyukan da ke jawo hankulan mutane a lokacin da ake mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Amma sabo da sharudan halitta masu tsanani na dutsen Qomolangma, shi ya sa ko za a iya kunna wutar gasar wasannin Olympics a kolin dutsen Qomolangma lami lafiya da kuma ci gaba da cin wutar ko a'a ya zama wani batu ne da ke jawo hankulan mutane sosai. Sabo da haka, kamfanin kimiyya da masana'antu na harkokin sararin samaniya na kasar Sin ya kafa wani sashen musamman don nazari da kuma kera wutar yola. Shao Wenqing, mataimakin babban mai zayyane-zayyane na sashen ya gaya mana cewa,

"Bisa kokarin da muka yi tare, kamar gwaje-gwajen da muka yi a cikin daki da waje, ciki har da gundumar Mohe da yake kuryar arewacin kasar Sin, da kuma zangon dutsen Qomolangma, da kuma gyare-gyaren da muka yi wa shirin wutar yola, yanzu muna iya tabbatar da cewa, za a iya kunna wutar yola da muka tsara a kolin dutsen Qomolangma."

Wata muhimmiyar matsalar fasaha da za a fuskanta lokacin da ake mika wutar gasar wasannin Olympics a dutsen Qomolangma ita ce yadda za a tabbatar da cin wutar da ke cikin fitila da kuma kunna wutar yola a wurin da tsayinsa ya yi yawa daga leburin teku a yanayin da ke da karancin iskar oxygen bisa sharudan zirga-zirga masu sarkakiya. Domin warware wannan matsala, sashen nazari da kuma kera wutar yola ya tsara wutar yola ta musamman da za a yi amfani da ita a dutsen Qomolangma da kuma daskararren makamashin wutar yola. Yin amfani da wannan daskararren makamashi zai iya tabbatar da kunna wutar yola lami lafiya ko da an gamu da mahaukaciyar guguwa. Qi Lei, mai zayyane-zayyane na sashen ya bayyana cewa, "Lokacin da muke tsara wannan makamashi, wani babban ci gaba da muka samu shi ne makamashin zai kone sannu sannu, kuma saurin konewarsa zai kai millimita 0.6 a ko wace dakika a kolin dutsen Qomolangma. Ban da wannan kuma, ta dimbin gwaje-gwajen da muka yi, an samu makamashin da ke hade da abubuwa daban dadan fiye da iri 100, kuma bayan da muka rinka yin gyare-gyare, mun samu wani irin makamashin da za a samu hayaki kadan lokacin da ake kunna shi."

Za a yi amfani da filitar wuta wajen kunna wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a kolin dutsen Qomolangma, shi ya sa yadda za a tabbatar da kunna wutar yola a kolin dutsen Qomolangma wata matsala ce da ke gaban kuniyar ba da tabbaci kan fasaha. Sabo da haka, sashen nazari da kuma kera wutar yola ta kamfanin kimiyya da masana'antu na harkokin sararin samaniya na kasar Sin ya tsara fitilar wuta ta dutsen Qomolangma ta musamman. Mr. Qi ya gaya mana cewa,

"Fitilar wuta ta dutsen Qomolangma ta yi amfani da daskararren makamashin da zai kone sannu sannu, wanda shi kansa yake da wasu sindarin oxidant. Ban da wannan kuma an kera fitilar wuta da kayayyakin kiyaye zafi, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba kawai ana bukatar iskar oxygen lokacin da ake kone ba, har ma ana bukatar kiyaye zafi. In ba haka ba, wutar za ta fi saukin kashewa."

Yanzu, an riga an mika wutar yola ta dutsen Qomolangma da kuma wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ga kungiyar hawa duwatsu da za ta mika wutar a dutsen Qomolangma, kowa yana jiran nasarar da za a samu wajen kai wutar yola zuwa kolin dutsen Qomolangma. Manazarta na sashen nazari da kuma kera wuotar yola suna da imani sosai kan nasarar da za a samu a cikin aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a dutsen Qomolangma.(Kande Gao)