
Ran 2 ga wata, Mr. Zhang Zhijian kakakin kungiyar 'yan hawa ta kasar Sin ya fayyace cewa, an riga an fara aiwatar da aikin mika wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing a kan tudun Qomolangma, yanzu 'yan hawa suna yin horo.

Mr. Zhang Zhijiang ya bayar da wannan labari a gun taron manema labaru da aka yi a zango na tudun Qomolangma. Kuma ya ba da labari cewa, an sa suna "mika wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing a kan tudun Qomolangma" ga wannan aikin mikawa, suna na kungiyar 'yan hawa shi ne "kungiyar 'yan hawa ta mika wutar yola ta wasannin Olympics a kan tudun Qomolangma".
Mr. Zhang Zhijiang ya fayyace cewa, yawan mutanen da za su mika wutar yola ya kai 50, yanzu suna zango na tudun Qomolangma. Amma Mr. Zhang Zhijian bai fayyace sunayen 'yan hawa da mutanen da za su mika wutar.
|