Ran 2 ga wata, an sami nasarar mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a yankin musamman na Hong Kong na kasar sin.
Hong Kong zango ne na farko a kan hanyar mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Sin, bayan da aka yi kwanaki 37 ana mika wa juna wutar a birane 19 na nahiyoyi 5 na duk duniya. Haka kuma, wannan na karo na 2 da Hong Kong ta yi maraba da wutar wasannin Olympic bayan gasar wasannin Olympic ta Tokyo a shekarar 1964.
An yi kimanin sa'o'i 7 ana mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a Hong Kong, tsawon hanyar mika wutar ya kai misalin kilomita 26, masu rike wutar 120 sun shiga aikin mika wutar. An mika wutar ta hanyoyin gudu da shiga kwale-kwale irin na gargajiya na kasar Sin da hawan doki. Madam Lee Lai-shan, wadda ta sami lambar zinariya ta farko ga Hong Kong a gun gasar wasannin Olympic ta zama mai rike wutar ta farko a wannan karo.
Bayan Hong Kong, za a kai wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a yankin musamman na Macao na kasar Sin.(Tasallah)
|