|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-05-02 13:47:23
|
|
Dangantakar da ke tsakanin kasashen Rasha da Georgia ta sake tabarbarewa
cri
Jiya, daya da watan Mayu, hukumar watsa labaru ta ma'aikatar tsaron kasa ta Rasha, ta sanar da cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar ta kara aikawa da su zuwa shiyyar Abkhazia ta kasar Georgia, sun riga sun isa wurin da aka nada da ke Abkhazia. A wannan rana kuma, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Georgia ta gabatar da takardar notis ga jakadan kasar Rasha da ke kasar Georgia, don kai kara kan lamarin. A sakamakon haka, dangantakar da ke tsakanin kasashen Rasha da Georgia ta sake tabarbarewa.
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha ta bayar da sanarwa a ranar 29 ga watan jiya cewa, za a kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya na Rasha da ke Abkhazia zuwa 3000. Sanarwar ta bayyana cewa, kasar Rasha ta dauki wannan mataki ne ba domin sarrafa shiyyar ba, amma don kiyaye babban ikon mazauna wurin ne. Bayan haka kuma, sanarwar ta la'anci kasar Georgia saboda ta yi jigilar makamai, da makamashi, da abinci, da kayayyakin soja zuwa kwarin Kodori, kuma ta tattara sojoji don shirin daukar matakan soja.
Bayan haka kuma, a gun wani taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergey Lavrov ya zargi kasar Georgia saboda kasar na da nufin warware matsalolin Abkhazia da na Kudancin Ossetia da karfin makamai. A waje daya kuma, ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayar da wata sanarwa, inda ta yi zargin cewa, kasar Georgia ta tsokana rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Rasha, kuma ta yi gargadin cewa, idan Georgia ta yi amfani da karfin soja, to, masu aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Rasha za su dauki matakai, don kiyaye zaman lafiyarsu da na shiyyar.
Kudurin da kasar Rasha ta tsaida game da kara aikawa da sojoji zuwa Abkhazia, ya gamu da adawa daga kasar Georgia, kuma ya jawo hankulan kasashen duniya.
Tun fil azal, ya kasance da bambanci da rikici a tsakanin kasashen Rasha da Georgia kan matsalolin Abkhazia da na Kudancin Ossetia. Abkhazia, wata jamhuriyar kasa ce mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta Georgia, a shekarar 1992 ta yi shelar samun 'yancin kai ita kanta, kuma ta yi rikicin soja tare da gwamnatin tsakiya ta Georgia. Kudancin Ossetia, wata jiha ce mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta Georgia, tana makwabtaka tare da kasar Rasha, da Arewacin Ossetia. Bayan da tsohuwar tarrayar Soviet ta rushe, shiyyar ta sanar da samun 'yancin kai, kuma tana adawa da gwamnatin tsakiyar Georgia cikin dogon lokaci. Ko da yake kasar Rasha ba ta amince da matsayin samun 'yancin kai na yankunan biyu, wato Abkhazia da Kudancin Ossetia a hukunce ba, amma a hakika dai, yankunan biyu suna samu goyon baya daga kasar Rasha a fannonin tattalin arziki da harkokin waje, kuma sun zama yankuna masu ikon aiwatar da harkokin kansu da suka samu 'yancin kai na gwamnatin tsakiya ta Georgia. Saboda haka, tun 'yan shekarun da suka wuce, kullum kasashen Rasha da Georgia su kan yi takaddama kan wanan batu.
Kazalika kuma, manazarta sun nuna cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen Rasha da Georgia ta sake tabarbarewa a kwanan baya, wannan na da nasaba da shelar samun 'yancin kai da Kosovo ta yi a watan Feburairu na shekarar da muke ciki. Bayan da Kosovo ta sanar da samun 'yancin kai, akwai labari na cewa, kasar Rasha za ta amince da 'yancin kai da Kudancin Ossetia da Abkhazia suka samu a matsayin daukar fansa kan kasashen Turai da Amurka don sun nuna goyon baya ga samun 'yancin kai na Kosovo.
|
|
|