Birnin Chong zuo dake kudancin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya shahara saboda ma'adinan Manganese ya ke da shi wanda nauyinsa ya kai Ton miliyan 150,wato a matsayin farko na kasar Sin. Kamfanin Eramet na kasar Faransa ya kafa wata masana'antar narke burabugan Mangnese wasu yan shekarun baya, aka tura Mr Johan Caretter,dan kasar Belgium zuwa kasar Sin domin daukar nauyin kafa masana'antar da tafiyar da harkokin masana'antar a matsayin manaja.
Kamfanin Eramet, babban kamfani ne na duniya wanda ya dukufa wajen ma'adinai da narke karafuna musamman wajen sarrafa bakin karfuna da hadaddun karafuna. A shekara ta 2004, kamfanin Eramet ya tsaida kudurin kafa masana'anta a birnin Chongzuo domin fitar batir na alkaline. A wannan shekara Mr Johan Carette yake da shekaru 43 da haihuwa aka tura shi zuwa kasar Sin domin share fage."Na zo nan kasar Sin ne a shekara ta 2004 bisa iznin da babban ofishin kamfanin Eramet ya danka mini na zabar wurin da za a kafa masana'antar, ya kuma mai da ni jami'in kula da shirin kafa masana'antar."
Mr Johan Carette ya ce yayin da ya fara zama a kasar Sin shi bai saba da shi ba. Ya ci gaba da cewa "matsala ta farko da nake fama da ita shi ne harshe. Da farko ba na iya magana da sinanci. Na yi sa'a ina da tafinta. Harshena Faransanci ne ba turanci ba ne. Da na sauka a nan, kamata ya yi in yi amfani da turanci wajen yin mu'amala. Komai na tafiya daidai, mun iya fahimtar juna na kammala aikina yadda ya kamata. A fannin abinci,abincin kasar Sin ya sha banban da namu kwarai da gaske, mutanen kasar Sin sun yi amfani da chopstick wajen cin abinci,wannan ya gagare ni sosai.
Bayan shekaru biyu da 'yan kai,mun kammala aikin share fage. Masana'antar da Mr Johan Caretter ya dau nauyin kafa ta ta fara aiki a watan Afrila na shekara ta 2007, da akwai ma'aikata wajen metan, jimlar kudin da aka zuba wajen kafa masana'antar ta kai kudin dalar Amurka miliyan talatin. Bayan da masana'antar ta fara aiki, aiki ya kan rufe Mr Johan. Ko wace rana ya yi aiki daga safe zuwa dare da karfe takwas ko tara. A ganin ma'aikatansa, Mr Johan shi mutumin da ya yi komai domin samu wani abu,kuma ya yi kokarin zama cikakke,ya yi aiki tare da kuzari sai ka ce shi agogo ne bai san gajiya ba. Johan ya ce kasar Sin ta samu saurin bunkasuwa, yana bukatar rubanya kokarinsa, ya yi amfani da damar nan ta bunkasuwa." Ya ce " A ganina da akwai fagagge da dama na bukatar bunkasa a kasar Sin,da yake wasu batutuwa ba su kai matsayin da ake bukata ba, amma mutanen kasar Sin suna iyakacin kokarinsu, wannan fiffiko ne da kasar Sin ke da shi. A Turai yayin da muka tabo batun bunkasa tattalin arzikin kasa, mu kan ce ci gaban tattalin arzikin kasa ya kai kashi biyu bisa dari a kowace shekara, amma a kasar Sin ana so a sarrafa ci gaban tattalin arzikin kasa cikin kashi goma bisa kashi dari. tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da kashi sama da takwas bisa dari a kowace shekara kuma yana da makoma mai haske."
Da akwai wani ra'ayi cikin falfasar gargajiya ta kasar Sin na cewa idan wani mutum yana so ya yi wani abu, sai ya yi shi bisa sauyin yanayin sararin samaniya da halin da ya sami kansa a ciki da kuma hadin kan jama'a. masana'antar da Johan Caretter ya kafa a birnin Chongzuo na jihar Guangxi ta samu ci gaba yadda ya kamata yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke samun ci gaba. Lalle ta amfana daga yanayin "doron kasa" da na "sararin samaniya" da kuma hadin kan jama'a. Abun da ya fi daukar hankalin Johan Carette shi ne ma'aikantansa na kasar Sin da dama sun zama aminansa wadanda suka bayar da taimako wajen fahimtar al'adun kasar Sin. Johan Carette ya ce " a cikin mu'amala da na yi da ma'aikatana sinawa, da yawa sun zama aminana. Muna aiki tare kuna tattaunawa tare mu kan baiwa juna labarai. Duk da haka da akwai siratsi a fannin al'adu,idan matasa ne babu siratsi da dama tsakaninmu a fannin al'adu, amma idan tsakanin wadanda suka fi shekaru sai da akwai siratsi mai yawa. A cikin shekaru uku da yake zama a kasar Sin, Johan Carette ya sa kafa a birane da dama na kasar Sin, ciki har da babban birnin kasar Sin Beijing wanda shi ne cibiyar harkokin siyasa da al'adu ta kasar Sin, da cibiyar tattalin arzki da kudade ta kasar Sin birnin Shanghai da tsohon babban birnin Sin Xi'an da biranen masana'antun dake arewancin kasar Sin Taiyuan da Datong da biranen dake bakin teku Dalian da Qingdao.sai ka ce ya ziyarci yawancin fadin kasar Sin. Kan biranen da ya kai ziyara, Johan yana da dogon bayani.ya ce ya ce "A ganina,birnin Nanning,birni mai launin tsanwa shur sabo da yawan bishiyoyi da ciyayi da yake da su a duk shekara kuma yanayi na da dan zafi,biranen Dalian da Qingdao suna da kyaun gani sosai,birnin Beijing birnin mai yawan al'adu idan kana so ka samu labaran ci gaban kasar Sin sai ka je sabon yankin Pudong na birnin Shanghai."
A kan matsayinsa mai kula da masana'anta yayin da yake zagaya a kasar Sin, Johan ya mai da hankalinsa wajen nazarin harkokin kasar Sin. Ya sa hankali kan matakan da kanana hukumomi na kasar Sin suka dauka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma sakamakon da suka samu, ya yi alfahari da saurin ci gaban da kasar Sin ta samu. Ya kuma ce yayin da yake karami, daga littattafai da hotuna ya samo labarai dangane da kasar Sin, yana dokin ganin kasar Sin. A wancan lokaci ya san kasar Sin wani mafarin tsohon al'adu a duniya,mutanen Sin su kan yi komai kafin sun yi dogon tunani. Da saukarsa a kasar Sin abin da ya ganam idonsa ya wuce abin da yake zata kan matakin da kasar Sin ke ciki wajen bude kofa ga kasashen waje da zamanintar da kasa. ya ce "Idan kana so ka fahimci kasar Sin, kamata ya yi ka sami kanka a cikin kasar Sin.Sa'ad da kake cikin kasar Sin ka iya fahimci kasar Sin. Wani al'ajabi shi ne kasar Sin ta fi sauran kasashe da bangare sauri wajen bunkasa tattalin arziki. Alal misali birnin Chongzuo inda masana'antarmu ke zaune, yayin da na sauka a nan ba haka yake ba. Birnin Chongzuo ya samu saurin cigaba." Johan ya ce wani abin musamman na kasar Sin shi ne mutanen kasar Sin suna aiki tukuru shi ya sa kasarsu ta samu saurin ci gaba. Ya kuma yaba wa kasar Sin kan manufar bude kofa ga kasashen waje da take bi.ya ce
"Manufar bude kofa ga kasashen waje,kyakkyawar manufa ce.ba ma kawai abun alheri ne ga kasar Sin ba hatta ma ga kasashen yamma,manufar nan ta amfanawa ci gaban kasar Sin sosai. A kasar Belgium kafa masana'anta ba aiki mai sauki ba ne kamar a kasar Sin, a kasar Sin aiki mai sauki ne idan kana so ka zuba jari a wannan kasa."
Ko da ya ke Mr Johan ba ya iya magana da harshen sinanci sosai ba, a ganin ma'aikatansa sinawa ya san al'amuran kasar Sin sosai. Madam Cai lanjuan, mataimakiyarsa ta ce "shi bako ne a kasar Sin amma ya shafe shekaru uku yana zama a kasar Sin. A ganina ya gane hanyoyin da sinawa ke bi wajen daidai harkokin yau da kullum. Alal misali yayin da muke mu'alla da 'yan kasuwa masu samar da kayayyaki, ko yayin da muke daddale kwangiloli, Mr Johan ya gane nufinsu, a ganina ya hada al'adun kasar Sin da na kasashen yamma."
Bayan da Johan ya sauka a kasar Sin ba da dadewa ba, ya kai iyalinsa a kasar Sin ya tsungunar da gidansa a birnin Shanghai. A halin yanzu kowane mako daga litinin zuwa juma'a yana aiki a birnin Chongzuo na jihar Guangxi,a karshen mako asaba da lahadi ya tafi birnin Shanghai ta jirgin sama ya hadu da iyalinsa. Johan ya ce iyalinsa na kaunar kasar Sin. Suna goyon bayansa kan aiki a kasar Sin.
Mr Johan yana kaunar silk da wasan opera na beijing na kasar Sin ya kan saye kayayyakin fasaha da alatun dake shaida alamun kabilun kasar Sin. Ya kan yaba zane zane masu kyaun gani da ke da halayen musamman na gabas. A cikin lokutan da yake zama a kasar Sin, halinsa na cin abinci ma ya canza a kwana a tashi. Abincin da ya fi so ci, shi ne gasasar naman agwagwan Beijing. Ya kan je dakunan sayar da abinci na birnin Chongzuo. Duk da haka ba ya saba da irin abincin da aka dafa da garin shimkafa kamar luwaidi da mutanen wurin su kan ci a lokacin karya kumallo.
Johan ya ce babban burinsa a halin yanzu shi ne masana'antarsa za ta samu ci gaba yadda ya kamata. Yayin da ya kammala hira da wakilinmu ,Johan ya yi amfani da sinanci ya ce ina kaunar kasar Sin, ina kaunar Chongzuo."
Jama'a masu sauraro, kun dai saurari wani bayani na game da yadda wani dan kasar Belgium Johan Caretter ya ke aiki da zama a kasar Sin. Wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na zaman rayuwar Sinawa. Mun gode muku saboda kun saurarenmu,to,sai wannan lokaci na mako mai zuwa za mu sake haduwa da juna.(Ali)
|